Rigimar APC ta zama danya, Kotu ta soke duka zaben shugabannin da aka yi a Anambra

Rigimar APC ta zama danya, Kotu ta soke duka zaben shugabannin da aka yi a Anambra

  • Lawrence Emegini da sauran shugabannin APC sun yi nasara a karar da suka kai jam’iyya a kotu
  • Alkali ya ce wa’adin Lawrence Emegini da duk shugabannin APC a Anambra bai kare ba har yanzu
  • Wannan ya sa kotu ta ruguza duka zaben shugabannin da jam’iyyar APC ta shirya kwanaki a Anambra

Anambra - Rigimar da ta bijirowa jam’iyyar APC a jihar Anambra ta rikida bayan da kotu ta ruguza zaben shugabannin da aka shirya a watan da ya wuce.

Jaridar Daily Trust ta ce wata babban kotu da ke zama a Awka, jihar Anambra ta rusa zaben APC.

Tsofaffin shugabannin APC 17 a karkashin jagorancin Lawrence Emegini suka kai jam’iyyarsu kotu, su na korafin cewa har zuwa yanzu wa’adinsu bai kare ba.

A kara mai lamba 2022 A/3/2022, tsofaffin shugabannin rikon kwarya na mazabu da kananan hukumomi sun kalubalanci ingancin zaben da aka gudanar.

Kara karanta wannan

2023: Masu neman takara 33 ke zawarcin tikitin gwamna na APC a wata jihar arewa

A ranar Laraba, 23 ga watan Fubrairu 2022, Alkalin babban kotun da ke zama a garin Awka, Ike Ogu ya zartar da hukunci, ya ba jam’iyyar APC rashin gaskiya.

Shugabannin APC
Andy Uba a fadar Shugaban kasa Hoto: pmnewsnigeria.com
Asali: UGC

An ba tsagin Emegini gaskiya

The Cable ta ce Mai shari’a Ogu ya yanke hukunci cewa APC ta dakata da shirya zabe kamar dai yadda Lauyoyin da suka tsayawa su Emegini suka bukata.

Kotu ta ce wa’adin shugabannin mazabu da na kananan hukumomi da na jihar da aka zaba a 2018 bai kare ba, don haka ba za a sauke su daga kan mukamansu ba.

Ike Ogu ya yi hukunci cewa duk wani zabe da APC ko wakilanta suka shirya a jihar Anambra, ya ci karo da doka, don haka sam shari’a ba ta san da zaman shi ba.

Kara karanta wannan

Kwankwaso, tsohon ministan Buhari: Jerin yan siyasar da suka kafa sabuwar kungiyar siyasa

Hukunci ya raba kan lauyoyi

Shugaban APC na bangaren ‘yan taware, Chukwuma Agufugo, ya ji dadin wannan hukunci. Haka zalika lauyan da ya kare su a kotu watau Cif P.I. Ikwueto (SAN).

A gefe guda, Chikwunoso Chinwuba wanda shi ne mai ba bangaren da ta sha kashi shawara, ya nuna za su daukaka wannan karar domin Alkalin ya yi kuskure.

A bar Ibo su yi mulki - Dr. Banire

A jiya ne aka fahimci Dr. Muiz Banire SAN ya ki goyon bayan takarar tsohon Ubangidansa, ya ce bai ma san har Bola Tinubu ya fara takarar shugaban kasa ba.

Banire yana goyon bayan Ibo su karbi mulki, kuma ya na ganin bai kamata duk wanda ya kai shekara 60 ya yi mulki ba, don haka Tinubu da Osinbajo sun tsufa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng