Dakta Banire: Nan gaba kaɗan jam'iyyar APC zata tarwatse saboda abu daya
- Tsohon mai ba da shawara kan harkokin doka na APC ta kasa ya ce APC ba zata jima ba nan gaba zata watse sabida abu ɗaya
- Ɗakta Muiz Banire, wanda tsohon kwamishinan shari'a ne a Legas, ya ce ginin da aka dora APC a kai ba mai ƙarko bane
- A cewarsa jam'iyyar APC ta bada fifiko mai tsoka ga gwaamnoni, kuma rashin haɗin kanta ne zai kai su ya baro
Lagos - Tsohon mai bada shawari kan harkokin shari'a na APC ta ƙasa, Dakta Muiz Banire, ya yi hasashen cewa nan bada jimawa ba jam'iyyar zata tarwatse.
Da yake jawabi a cikin wani shirin gidan Radiyo dake jihar Lagos, Banira ya bayyana cewa kowa yasan APC tasaba yi wa doka karan tsaye.
Ya ce duk wata kungiya ko tawaga da take saba wa dokoki, ba zata taɓa yin tsawon rai ba, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
A cikin tattaunawar, Tsohon kwamishinan shari'a a jahar Legas, Banire ya ce:
"Babu tantama jam'iyyar APC za ta watse. Mutane kala daban-daban sun haɗu wuri ɗaya domin su samu mulki amma sun gaza haɗa kan su wuri ɗaya. Rikici na ƙara raba jam'iyyar."
Menene abun da zai watsa APC?
Masanin shari'a ya kara da cewa an gina tubalin jam'iyyar APC da kaso mai tsoka a hannun gwamnonin da suka samu mulki karkashinta.
Wannan dalilin ne yasa shugaban kwamitin rikon kwarya, Gwamna Mala Buni, ya amince da tsagin shugabannin APC na gwamnoni a jihohi.
Ya kuma bayyana cewa ya yi iyakacin kokarinsa wajen dawo da jagorancin APC kan hanyar doka a matsayinsa na mashawarcin doka na ƙasa amma suka rufe kunnuwan su.
Dakta Banire ya ce ya tsame kansa bayan wa'adinsa ya kare saboda gano cewa bai ɗauki hanyar da zata ɓulle ba.
A wani labarin na daban kuma Gwamnan PDP ya sallami shugaban ma'aikatan fadar gwamnati daga aiki
Gwamnan jahar Akwa Ibom ya sallami shugaban ma'aikatan fadar gwamnatinsa daga bakin aiki ranar Talata.
Rahoto ya nuna cewa sabanin siyasa ne ya shiga tsakanin kusoshin jihar kuma ya yi awon gaba da kujarar ta Chief Of Staff.
Asali: Legit.ng