2023: Matasa a yankin Kudu sun nace, sun nemi Atiku ya bayyana kudurinsa na takara
- Kungiyar matasa a yankin kudancin kasar sun nuna goyon bayansu ga takarar Atiku Abubakar a zaben shugaban kasa na 2023
- Kungiyar mai suna SOYA ta nemi Atiku ya ayyana aniyarsa na takara ko kuma tayi masa kallon matsoraci
- Ta ce kasar na bukatar mutum mai fadar gaskiya kuma wanda zai magance matsalolinta
Ogun - Matasa a yankin kudancin kasar sun bukaci tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar da ya ayyana aniyarsa na yin takarar shugaban kasa a zaben 2023 ba tare da ci gaba da bata lokaci ba.
Kungiyar karkashin inuwar Southern Youth Alliance (SOYA) ta sha alwashin kallon ci gaba da shirun Atiku kan Shugabancin 2023 a matsayin tsoro, Daily Trust ta rahoto.
Shugaban kungiyar SOYA, Ismail Ridwan, ya bayyana hakan a Abeokuta, jihar Ogun, a yayin wani taron manema labarai da kungiyar ta shirya don marawa kudirin tsohon mataimakin shugaban kasar baya.
Ridwan tare da sauran mambobin kungiyar sun rike kwalayen sanarwa dauke da rubutu kamar haka:
“Shekaru dama ce ga Atiku”, “Atiku na kaunar matasa.” “PDP ta hau tudun na tsira da Atiku”, Atiku Shugaban kasa a 2023”, “Atiku ya yiwa matasa alkawarin kaso 40 cikin 100 a gwamnati”, “Najeriya za ta tsira a hannun Atiku.”
Shugaban kungiyar ya bayyana cewa a matsayinsu na kungiyar matasa, sun goyi bayan matasa a mukaman shugabanci, amma cewa ya kamata a fi mayar da hankali kan shugabanci na cancanta.
Ya kuma bayyana cewa Najeriya na kewaye da tarin matsaloli na rashin tsaro, talauci, da yawan bashi cewa kasar na bukatar shugaba da zai iya fadin gaskiya da kawo gyara.
Daily Trust ta nakalto yana fadin:
“Hankalinmu bai kwanta da shirun Atiku wajen ayyana aniyarsa na takarar zaben Shugaban kasar ba. Idan bai aikata haka ba, za mu yarda cewa shi matsoraci ne, za mu yarda cewa yana jin tsoro.
“Muna mika bukatarmu cikin mutunci cewa mai girma Atiku Abubakar ya yi magana kan kudirinsa na takarar shugaban kasa a zaben 2023 sannan ya ayyana aniyarsa don tabbatar da hakan.”
Ya kuma nuna rashin nutsuwar kungiyar kan adawar da ake yi da Atiku, cewa shekaru bai da alaka da shugabanci.
Zaben 2023: Kotu ta kori karar da ke kalubalantar cancantar Atiku na tsayawa takara
A gefe guda, wata babbar kotun tarayya da ke birnin Abuja, ta yi watsi da karar da ke kalubalantar cancantar tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar na neman takarar kujerar shugaban kasa.
Da yake zartar da hukunci a ranar Litinin, 21 ga watan Fabrairu, Justis Inyang Ekwo, ya yi watsi da karar kan hujjar cewa bangaren da ya shigar da karar bai da yancin yin hakan.
Justis Ekwo ya bayyana mai karar a matsayin mai shiga sharo ba shanu, Punch ta rahoto.
Asali: Legit.ng