Tsohon Kwamishinan Ganduje bai dandara ba, ya dawo Facebook daga barin kurkuku

Tsohon Kwamishinan Ganduje bai dandara ba, ya dawo Facebook daga barin kurkuku

  • Kwanakin baya ne aka ji an tsare Injiniya Mu’az Magaji yayin da ake shari’a da shi a gaban Alkali
  • Tsohon kwamishinan ayyukan na jihar Kano ya samu ‘yancin-kai bayan Alkali ya bada belinsa
  • A daren yau ‘Dansarauniya ya cigaba da amfani da shafin Facebook kamar yadda ya saba a baya

Kano - An shafe kusan makonni biyu ba tare da an ji duriyar Mu’az Magaji wanda aka fi sani da ‘Dansarauniya a dandalin sada zumunta na Facebook ba.

Dalilin kuwa shi ne ana ta faman shari’a da Injiniya Mu’az Magaji, wanda har ta kai an tsare shi.

A yammacin Laraba, 16 ga watan Fubrairu 2022 kewan da masoya suke yi wa Mu’az Magaji ya zo karshe, aka ga ya fito shafinsa a Facebook, ya yi magana.

Kara karanta wannan

Akwai wasu irin Abba Kyari a cikin Rundunar 'Yan Sanda, AIG Iwar Mai Ritaya

Da kimanin karfe 8:20 na dare ne Jagoran tafiyar Win-Win ko Kano sabuwa a siyasar Kano watau ‘Dansarauniya ya yi maganar farko a shafinsa tun a Junairu.

‘Dan siyasar ya shafe kwanaki 20 rabonsa da Facebook, abin da ba a saba gani daga wurinsa ba. A ranar 27 ga watan Junairu ya yi maganar karshe a shafinsa.

Mu’az Magaji ya rubuta ‘Testing’ a shafinsa, ma’ana ya na sharan fage domin ya cigaba da magana a dandalin zamanin kamar yadda ya saba kafin ya shiga hannu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Tsohon Kwamishina da Ganduje
Mu’az Magaji da Gwamna Ganduje Hoto: dailynigerian.com
Asali: UGC

Na dawo da karfi na

Daga baya kuma sai aka ga ‘Dan sarauniya ya rubuta: “Alhamdulillahi. Came out Stronger & much more determined.”

Abin nufi dai ya na godiya ga Ubangiji (SWT), ya kuma ce ya dawo da karfinsa da kwarin gwiwar jajircewa.

A maganganun da ya yi cikin daren na yau, jigon na APC a Kano ya godewa dinbin mutanen da suka nuna masa kauna lokacin da ya ce ya je sauke faralin siyasa.

Kara karanta wannan

Yajin-aiki: Kungiyar Dalibai ta fadi matakin da za ta dauka kan ASUU da Gwamnatin Buhari

Magaji ya mika godiyarsa ta musamman ga ‘dan jaridar nan, Jafar Jafar da dawainiya da ya yi da tafiyarsa a kafafen zamani da kuma lauyansa, Garzali Datti.

Jagoran Win Win ya yi godiya

“Godiya ta musanman ga acting Jagora, Kuma Coordinatan Win Win Kano sabuwa da dukkan magoya baya dake kasashen waje. Tare da abokan arzuka!”
“Godiya ga Allah SWT, Godiya ga iyalina, Yan Uwa, Abokai da magoya baya...godiya ta musanman ga Bar Garzali Datti tareda abokan aikinsa! It's a win win”

A cewar Magaji, burinsa na ganin an daura jihar Kano a kan sabuwar turba ta na daf da kai ga ci.

Bayan kusan shafe sa’a guda, a daidai karfe 9:43 sai Injiniya Magaji ya yi sallama da mutanen Facebook bayan ya yi ta wallafa wasu hira da aka yi da shi.

Shari'ar Dansarauniya

Da ake shari’a da ‘dan siyasar, kun ji cewa dole kotu ta ɗage sauraron karar tsohon kwamishinan ayyukan saboda kararsa ta yi karo da shari'ar Sheikh Abduljabbar Kabara.

Kara karanta wannan

Harkar kwayoyi: Abin da ya dace IGP ya yi wa Kyari ba tare da bata lokaci ba - Lauya

A wancan lokaci, Lauyan tsohon kwamishinan ya ce duba da dalilin da aka kawo, sun rungumi kaddara. Hakan ta sa Muaz Magaji ya kara wasu 'yan kwanaki kafin ya fito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng