2023: Wata Ƙungiya Ta Sake Shawartar Atiku Ya Haƙura Da Batun Sake Fitowa Takarar Shugaban Ƙasa

2023: Wata Ƙungiya Ta Sake Shawartar Atiku Ya Haƙura Da Batun Sake Fitowa Takarar Shugaban Ƙasa

  • Wata kungiyar kudu maso yamma ta shawarci Atiku Abubakar akan ya hakura da batun tsayawar sa takara a zaben 2023 da ke karatowa
  • A cewar Olufemi Osabinu, jigon kungiyar, ba zai yuwu dan arewa ya ci gaba da mulkar kasa ba bayan Shugaba Buhari ya kammala shekaru 8 a mulki
  • Kungiyar ta kara da bayyana batun shekarun tsohon mataimakin shugaban kasar, inda tace akwai bukatar mai jini a jika ya amshi mulki ba shi ba

Jihar Legas - Dangane da zaben shugaban kasa na 2023 da ke karatowa, an bai wa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar shawarar hakura da takara don samun zaman lafiyar kasar nan.

Vanguard ta ruwaito yadda kungiyar South-West Development Frontier (SDF), ta mika wannan bukatar gare shi a ranar Litinin, 14 ga watan Fabrairu inda tace arewa ba za ta ci gaba da mulkin kasa ba bayan Shugaba Muhammadu Buhari ya kammala shekaru 8 a kujerar mulki.

Kara karanta wannan

2023: Atiku Ya Magantu Game Da Batun Karɓa-Karɓa a Mulkin Najeriya

2023: Ka Hakura Da Takarar Shugaban Kasa, Kungiyar Kudu Maso Yamma Ga Atiku
2023: Kungiyar Kudu Maso Yamma Ta Bukaci Atiku Ya Hakura Da Batun Sake Yin Takarar Shugaban Kasa. Hoto: Atiku Abubakar
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Olufemi Osabinu, jagoran kungiyar ya ce Atiku ya yi wa kasa aiki a baya don haka ya kamata ya ba wa yara masu jini a jika damar shugabanci don kawo karshen rashin tsaron da ke addabar kasar nan, kamar yadda The Cable ta rahoto.

A cewarsa ya kamata a yi adalci ga yankunan kasar nan

Yayin jawabi a wata zanga-zanga da aka yi a Legas, ya kula da yadda masu goyon bayan Atiku ya yi shugabanci suke kokarin kawo rashin adalci ga kasar nan wanda zai kawo rabuwar kawuna.

Ya ci gaba da cewa a bar ‘yan Najeriya su zabi shugaban da zai ciyar da kasa gaba ya kuma dasa daga inda wannan mulkin ya tsaya.

Kungiyar ta ce akwai bukatar a yi tsarin karba-karba don kawo hadin kai a kasa da kuma warkar da ciwon da ke zuciyoyin jama’a.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: Jonathan Ya Goyi Bayan Gwamnan PDP Ya Zama Shugaban Ƙasa a 2023

A cewarsa shekarun Atiku 77 don haka ya wuce ya yi shugabanci

A cewar Osabinu:

“Muna kira ga tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar akan ya sauya tunani dangane da burinsa na kara tsayawa takara a 2023.
“Yayin da Atiku ya rike mukami a kasar nan, maganar gaskiya shi ne mun dade muna mara masa baya, amma shekarun sa 77 don haka bai dace da shugabanci ba.”

2023: Magoya bayan Atiku sun buƙaci ya haƙura da takara, ya goyi bayan ɗan takara daga kudu

A baya, Gamayyar kungiyoyin masu goyon bayan tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar sun shawarci Turakin na Adamawa ya hakura da yin takarar shugaban kasa a 2023 amma ya goyi bayan dan takara daga kudu maso gabashin kasar.

Kungiyoyin sun hada da Middle Belt Network for Atiku, North For North Support Group for Atiku, Turaki Arewa Vanguard for Atiku da South-West Development Frontiers, The Cable ta ruwaito.

Kara karanta wannan

2023: Magoya bayan Atiku sun buƙaci ya haƙura da takara, ya goyi bayan ɗan takara daga kudu

Atiku bai riga ya bayyana cewa zai fito takarar shugaban kasar ba a hukumance amma ana hasashen yana shirin sake neman kujerar shugaban kasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164