Shugaba Buhari ya watsa wa gwamnonin APC biyu ƙasa a ido, ya ƙi amincewa da bukatarsu
- Shugaba Buhari ya watsa wa wasu gwamnonin APC biyu ƙasa a Ido, ya umarci su bi matakai matukar suna son ya amince
- Rahoto ya nuna cewa gwamnonin sun garzaya ga Buhari ne domin ya goyi bayan ɗan takarar da suke so ya zama shugaban APC
- Wannan lamari dai bai yiwa sauran gwamnoni daɗi ba, inda suka shirya zama dan tsara yankunan da za'a kai kujerun jam'iyya yau
Abuja - Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya yi watsi da shirin gwamnonin APC biyu na ya ɗauki wani ɗan takara a matsayin shugaban jam'iyya na gaba yayin babban taron dake Tafe.
A rahoton The Nation, Buhari ya bukaci gwamnonin guda biyu, su kai shawarinsu gaban kwamitin rikon kwarya, takwarorinsu gwamnoni, da masu ruwa da tsaki domin duba yuwuwar haka.
Wannan yunkurin cusa wa Buhari ra'ayin wani ɗan takara ta bayan fage, ya jawo sabon rikici a kungiyar gwamnonin APC, waɗan da ke shirin zaman kasafta kujerun jam'iyya zuwa yanki-yanki.
Wata majiya ta shaida cewa duk abin da gwamnonin suka cimma yayin ganawarsu, za su gabatar wa shugaba Buhari domin ɗaukar matakin karshe.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Lamarin dai ya fusata da yawa daga cikin gwamnonin APC da mambobin kwamitin rikon kwarya, kasancewar an yi yunkurin cusa wa Buhari wani ɗan takara, kamar yadda Leadership ta rahoto.
Suwa ke neman kujerar shugaban APC?
Zuwa yanzu, waɗan da ke neman kujerar shugabancin APC sun haɗa da tsohon gwamnan Zamfara, Abdul'aziz Yari, Mallam Saliu Mustapha, tsohon gwamna, Umar Tanko Al-makura.
Sai kuma Sanata Sani Muhammad Musa, tsohon gwamna, Ali Modu Sherrif, Sunny Sylvester Monidafe, Mohammed Etsu, tsohon gwamna, George Akume, Isa Yuguda da Dakta Sani Abdullahi Shinkafi.
Sauran dake neman wannan kujera su ne, tsohon gwamna, Abdullahi Adamu, da kuma ɗan majalisar dokokin tarayya, Honorabul Bawa Bwari.
Bincike ya nuna cewa uku daga cikin gwamnonin 22 na APC sun amince su kaiwa shugaba Buhari shawarin ɗan takarar da suke kaunar ya zama shugaba.
Suwa ye suka kai wa Buhari ɗan takara?
Biyu daga cikin wannan gwamnonin uku sun fito daga yankin Arewa, yayin da ɗaya kuma daga kudu.
Gwamnonin biyu na arewan sun garazaya ganin shugaban ƙasa Buhari da nufin cusa masa ɗan takarar da suke kauna, ɗaya daga cikin su na hangen kujerar mataimakin shugaban ƙasa a 2023.
Wata majiya ta ce:
"Gwamnonin sun ziyarci fadar shugaban ƙasa, da nufin yi wa yan uwansu kwantan bauna a siyasa, amma Buhari ya ƙi amince wa da shawarin su."
"Ya faɗa wa gwamnonin su tura shawarar su ga kwamitin rikon kwarya tun da akwai shugabanci a jam'iyya, su bi ta hanyar da ya dace domin turo sakon su. Ba su san Buhari ɗan ka'ida bane."
"Gwamnonin ba su sami nasara a manufarsu ba, kuma sun gaza komawa ga takwarorin su. Da yawan gwamnonin APC ba su ji daɗin haka ba."
A wani labarin kuma gwamna Tambuwal ya bayyana abu ɗaya da ya rage wa Buhari matukar yana son yan Najeriya su rinka tunawa da shi
Gwamnan Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, yace abu ɗaya ya rage wa shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya aiwatar kafin ya bar mulki.
Tambuwal ya ce gudanar da tsaftataccen zaɓe mai inganci a 2023 ne kaɗai ya rage wa shugaban INEC da shugaba Buhari.
Asali: Legit.ng