Abu ɗaya muke bukatar shugaba Buhari ya aiwatar kafin ya miƙa mulki a 2023, Tambuwal
- Gwamnan Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, yace abu ɗaya ya rage wa shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya aiwatar kafin ya bar mulki
- Tambuwal ya ce gudanar da tsaftataccen zaɓe mai inganci a 2023 ne kaɗai ya rage wa shugaban INEC da shugaba Buhari
- Ya faɗi haka ne yayin da ya kaiwa tsohon gwamnan Kaduna, Ahmed Makarfi, Ziyara ta neman shawara a takararsa
Kaduna - Gwamna Tambuwal na jihar Sokoto, yace abu ɗaya da ya rage shugaban ƙasa, Buhari, ya gudanar shi ne sahihi kuma karbabben zabe a 2023.
Jaridar Punch ta rahoto Tambuwal na cewa ya kamata shugaba Buhari ya yi koyi da tsohon shugaban ƙasa, Goodƙuck Jonathan, wajen tabbatar da an gudanar da sahihin zaɓe.
Gwamnan ya yi wannan furucin ne yayin zantawa da manema labarai jim kaɗan bayan ziyarar da ya kaiwa tsohon gwamnan Kaduna, Sanata Ahmed Maƙarfi, a Kaduna ranar Alhamis.
Tambuwal ya kai ziyarar ne bisa rakiyar tsohon gwamnan Sokoto, Attahiru Bafarawa, da tsohon ministan albarkatun ruwa, Mukhtar Shagari.
Sauran waɗan da suka marawa gwamna baya zuwa Kaduna sune, yan majalisar dokokin Sokoto, sojojin da suka yi ritaya da jiga-jigan PDP na jahar Sokoto.
Meyasa yake bukatar gwamnati ta gudanar da zaɓe mai tsafta?
Game da zaɓen dake tafe, Tambuwal ya bukaci shugaban INEC, Farfesa Mahmud Yakubu, ya shirya sahihi, ingantacce kuma zaɓe mai tsafta domin ya bar baya mai kyau gare shi da shugaban ƙasa.
Tambuwal ya ce:
"Shugaban ɓangaren zabe ba shi da wani zaɓi da ya wuce ya bar abin da za'a tuna da shi, kuma a iya sani na ya fito daga gidan mutunci mai tarihi."
"Dan haka zai yi taka-tsantsan wajen tabbatar da bai ɓata tarihin gidansu ba, da tarihin shi kansa, wajen shirya sahihi kuma ingantaccen zaɓe."
"Ko shugaban ƙasa Buhari duk da gazawar da muke ganin ya yi, abu ɗaya da ya rage masa wanda za'a rika tuna wa da shi, shine ya tabbatar da an yi zaɓe mai tsafta kuma sahihi."
A wani labarin kuma Gwamna Tambuwal ya kai ziyara jihar Katsina. ya zaygana wasu matsaloli da Najeriya zata sake shuga idan APC ta zarce 2023
Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, ya ce tattalin arziki da tsaro zasu faɗi warwas matukar aka bari APC ta cigaba da jagorancin Najeriya a 2023.
Yace gwamnatin APC karkashin shugaba Buhari ta kawo wa yan Najeriya rashin tsaro, faɗuwar tattalin arziki da lalacewar harkokin lafiya.
Asali: Legit.ng