2023: Gwamnan PDP dake son gaje Buhari ya shiga Katsina, ya jero matsalolin da za'a shiga idan APC ta zarce
- Gwamnan Sokoto, Aminu Tambuwal, ya kai ziyara jihar Katsina a cigaba da neman shawara da goyon baya kan takararsa a 2023
- Tambuwal yace matukar yan Najeriya suka sake APC ta zarce kan madafun iko, tattalin arziƙi da tsaro zasu kara lalacewa a faɗin kasa
- Yace da zaran ya ɗare kan mulkin kasa a 2023, zai kafa gwamnatin da zata jawo kowa a jiki
Katsina - Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, ya ce tattalin arziki da tsaro zasu faɗi warwas matukar aka bari APC ta cigaba da jagorancin Najeriya a 2023.
This Day ta rahoto gwamnan na cewa gwamnatin APC karkashin shugaba Buhari ta kawo wa yan Najeriya rashin tsaro, faɗuwar tattalin arziki da lalacewar harkokin lafiya.
Tambuwal ya ƙara da cewa matukar mutane suka yi sake jam'iyyar APC ta cigaba da jagoranci har bayan 2023, to ƙasar nan zata iya tarwatse wa.
Gwamnan Tambuwal ya yi wannan jawabin ne a garin Katsina, inda yaje tattaunawar neman shawari da goyon bayan masu ruwa da tsaki na PDP a jihar.
Wajibi mu haɗa kai don ceto Najeriya - Tambuwal
A cewar gwamnan Katsinawa sun san halin rashin tsaron da ake ciki, su ya dace su labarta wa yan Najeriya taɓarɓarewar tsaro.
A jawabinsa ya ce:
"Ya zama wajibi mu yi aiki tukuru mu haɗa kan mu domin kwace mulki daga hannun wannan gwamnatin. Wajibi mu haɗa kai a jam'iyyance mu ceto Najeriya."
"Bamu taba shiga matsanancin talauci a ƙasar nan ba irin yadda muke gani yanzu. Tattalin arziki ya lalace, tsaro kuma ba'a maganar shi."
"Mutanen Katsina ganau ne ba jiyau ba, ku ya dace ku faɗa wa sauran yan Najeriya muhimmancij tsaro gare su idan akwai."
Zamu tafi da kowa idan muka hau mulki
Ya bayyana cewa idan yan Najeriya suka zaɓe shi a 2023, zai gudanar da gwamnatinsa a buɗe, kuma zai tafi da kowa.
Yace gwamnatin zata haɗa kai da ɓangaren masu zaman kansu kuma ta samar da ingantaccen tsaro domin baiwa manoma damar koma wa sana'ar su.
A wani labarin kuma Kotu ta yanke hukuncin karshe game da dauya shekar gwamna Matawalle zuwa jam'iyyar APC
Babbar Kotun tarayya dake Gusau, ta yi fatali da ƙarar da aka shigar gabanta kan sauya shekar gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara.
Alkalin Kotun, Mai Shari'a Aminu Aliyu, yace Kotu ba ta da hurumin shiga lamarin siyasa da ya shafi jam'iyyu.
Asali: Legit.ng