2023: Manyan jiga-jigan PDP a Jigawa sun marawa dan Lamido baya don samun tikitin gwamna na jam’iyyar

2023: Manyan jiga-jigan PDP a Jigawa sun marawa dan Lamido baya don samun tikitin gwamna na jam’iyyar

  • An nemi Mustapha sule Lamido ya shiga tseren kujerar gwamnan Jigawa na 2023 a karkashin inuwar jam’iyyar PDP
  • Kungiyar tsoffin shugabannin kananan hukumomi na jam’iyyar adawar ne suka bukaci hakan
  • Mustapha ya kasance da ga tsohon gwamnan jihar, Alhaji Sule Lamido

Jigawa - Kungiyar tsoffin shugabannin kananan hukumomi na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a jihar Jigawa sun yi kira ga Mustapha Sule Lamido da ya shiga tseren kujerar gwamna a zaben 2023 karkashin inuwar jam’iyyar.

Kungiyar ta yi kiran ne a cikin wata takarda da ta saki a yayin taronta da ya gudana a garin Gumel da ke jihar Jigawa, Leadership ta rahoto.

Sanarwar wacce sakataren kungiyar kuma tsohon shugaban karamar hukumar Yankwasi, Hon Musa Abdullahi Karkarna, ya karanto, ta ce shugabannin kananan hukumomi 22 cikin 27 da suka yi aiki a gwamnatin PDP sun halarci taron.

Kara karanta wannan

Guguwar sauya sheka: Ana gab da yiwa APC mai kankat gabannin 2023 - Tambuwal

2023: Manyan jiga-jigan PDP a Jigawa sun marawa dan Lamido baya don samun tikitin gwamna na jam’iyyar
2023: Manyan jiga-jigan PDP a Jigawa sun marawa dan Lamido baya don samun tikitin gwamna na jam’iyyar Hoto: @mansurahmed09
Asali: Twitter

Ya kuma ce dukkansu sun amince cewa yakamata Mustapha, dan tsohon gwamnan jihar, Alhaji Sule Lamido, ya rike tutar jam’iyyar a zaben gwamna mai zuwa.

Mustapha ne zai iya ceto jihar daga halin da take ciki

Ya bayyana cewa kungiyar ta zauna ta yi nazarin halin da jihar Jigawa ta tsinci kanta ciki a yau, sannan ta bayyana cewa jihar na fama da matsalolin zamantakewa da na tattalin arziki da kuma tabarbarewar ababen more rayuwa wanda ke bukatar gyara.

Rahoton ya kara da cewar kungiyar ta kuma riki cewa ta hango duk wasu abubuwan da ake bukata daga wanda zai iya aikin gyara jihar Jigawa a tattare da Dr Mustapha Sule Lamido.

Kungiyar ta ce:

“Mustapha Sule Lamido na da ilimi sosai kuma yana da karfin zuciyar tunkarar hukunci mai tsauri a mawuyacin lokaci sannan ga shi da gaskiya kuma dan jam’iyya ne mai biyayya, don haka muna ganin zai iya yin wannan aiki.

Kara karanta wannan

2023: Hotunan ziyarar da manyan jiga-jigan PDP suka kaiwa tsohon shugaban kasa, IBB

“A kan haka, muna kira ga wannan matashi kuma salihi wato Mustapha Lamido da ya fito yayi takarar tikitin gwamnan wannan jam’iyya tamu ta PDP mai albarka domin shirin ceto.”

Guguwar sauya sheka: Ana gab da yiwa APC mai kankat gabannin 2023 - Tambuwal

A wani labarin, gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, ya ba jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) tabbacin cewa kwanan nan za ta tarbi masu sauya sheka daga sauran jam’iyyun siyasa gabannin zaben 2023.

Tambuwal ya bayyana hakan ne a ranar Talata, 8 ga watan Fabrairu, yayin ziyararsa ta uku kan neman shawara game da kudirinsa na neman tikitin shugaban kasa na PDP a Birnin Kebbi, jihar Kebbi, jaridar The Nation ta rahoto.

Gwamnan ya ziyarci Bamaina a jihar Jigawa da Gusau a jihar Zamfara tun a makon da ya gabata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng