Zaben 2023: Duk jam'iyyar da ta tsayar da ɗan arewa ba zata samu nasara ba, Gwamnan APC
- Gwamnan jihar Ondo ya ƙara jaddada matsayar gwamnonin kudu cewa wajibi ne a baiwa ɗan kudu kujerar shugaban ƙasa a 2023
- Rotimi Akeredolu, ya ce matukar ana son yin adalci da kuma dai-daito to bayan shekara 8 a arewa kamata ya yi mulki ya koma kudu
- Yace gwamnonin kudu sun riga sun yanke hukunci, duk wanda aka tsayar daga yankin kudu to shi zasu antaya wa kuri'u
Ondo - Shugaban ƙungiyar gwamnonin kudu kuma gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu (SAN), ya yi gargaɗin cewa duk jam'iyyar da ta tsayar da ɗan arewa a takarar shugaban ƙasa ba zata yi nasara ba.
Daily Trust ta rahoto cewa gwamnan ya yi wannan furucin ne a ofishinsa, yayin da ya karɓi baƙuncin kungiyar Power Rotation Movement, bisa jagorancin shugaba, Dakta Pogu Bitrus.
Akeredolu yace duk ma su nuna adawa da tsarin mulkin karɓa-karba to ba su ƙaunar Najeriya ta cigaba da zama ƙasa ɗaya kuma tsintsiya ɗaya.
TVC News ta rahoto Ya ce:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"A taron da muka yi biyu zuwa uku, mun bayyana cewa wajibi a miƙa mulki yankin kudu. Jam'iyyar da ba zata yi nasara ba ita ce zata tsayar da ɗan takara daga Arewa."
"Ku nan yanzu tafiya ce ta mambobin jam'iyyun siyasa daban-daban da suka haɗa kansu, abin da yake matsayar mu shi ne a yi ɗai-daito wajen tsarin karba karba."
"Abu ɗaya da za'a yi wajen tabbatar da adalci da kuma daidaito shine mulki ya yi shekara 8 a hannun dan arewa, to a miƙa shi hannun wani ɗan Kudu."
Menene matsayar gwamnonin Kudu?
Kazalika gwamna Akeredolu ya jaddada cewa shi da yan uwansa gwamnonin kudu bakin su ɗaya, duk wanda aka tsayar ɗan kudu shi za su goya wa baya.
"Wasu na cewa kamata ya yi a duba cancanta game da shugaban ƙasa, shin suna nufin ba bu wanda ya cancanta ne a Kudu?"
"Yan uwana gwamnonin kudu duk bakin su ɗaya, duk wanda aka tsayar a kudu shi za su goya wa baya. Mun faɗa mun ƙara faɗa wajibi shugaban kasa na gaba ya fito daga Kudu."
A wani labarin kuma Gwamnan Arewa dake son gaje kujerar Buhari ya shiga Kebbi, ya samu gagarumin goyon bayan PDP
Gwamna Aminu Tambuwal na jihar Sokoto ya kai ziyara jihar Kebbi game da kudirinsa na neman shugaban ƙasa a 2023.
Gwamnan ya gana da shugabannin PDP na jihar, kuma sun amince sun tabbatar masa da goyon bayan ya dare kujera lamba ɗaya.
Asali: Legit.ng