Babbar magana ta fito: Shugaban PDP na jihar Kudu ya sauya sheka zuwa APC, ya fadi sirri
- Shugaban jam’iyyar PDP a karamar hukumar Udu ta jihar Delta, Henry Ughwujowhovwo, ya sauya sheka zuwa APC
- Ughwujowhovwo ya yi zargin cewa son zuciya na ruguza jam’iyyar ba tare da sanin Gwamna Ifeanyi Okowa ba
- Ya kuma yi zargin cewa an mayar da wadanda suka yiwa jam’iyyar adawar hidima saniyar ware
Shugaban jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a karamar hukumar Udu da ke jihar Delta, Mista Henry Ughwujowhovwo, ya sauya sheka zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki.
Ughwujowhovwo ya bayyana karanta da son zuciya na wasu shugabanni a matsayin dalilinsa na ficewa daga jam’iyyar, inda yayi gargadin cewa PDP na durkushewa a Udu amma ba a fada ma gwamnan gaskiya, Independent ta rahoto.
Da yake jawabi a yayin sanar da komawarsa APC a hukumance, tsohon shugaban na PDP ya bayyana cewa zuwa 2023, wadanda ke da kasar za su tabbatar da karfinsu ta hanyar kuri’un da za su jefa, inda ya ce babu wani dalili na yin tinkawo amma za a gani a kasa.
Ya kuma bayyana cewa wadanda ke son barin PDP a Udu sun fi masu yiwa jam’iyyar biyayya yawa.
Ya ce:
"Lamuran siyasa yanzu yana zagaye ne a wuri daya. A shekarar 2023, wadanda ke cikin wannan rukuni, wadanda suka janye dukkan alfanun gwagwarmayar bayan babban zabe za su je su tabbatar da karfinsu a fagen daga.
“Zamanin wani da aiki, wani da ci ya wuce. Da yawa daga cikin wadanda suka yiwa jam’iyyar bauta an mayar da su tamkar saniyar ware yayin da wadanda suka yi adawa da jam’iyyar a 2019 sune ke shan romon dadi a wajen mutanen da ke kewaye da gwamnan.
“Gwamnan na yarda da duk wasu karairayi da aka fada masa kuma 2023 zai zamo shekarar azaba ga wadanda basa yiwa makwabtansu fatan alkhairi. Nade-naden mukaman siyasa na gefe daya da gwamnatin jihar Delta karkashin jagorancin Okowa ke yi da kuma wasu munanan dabi’un siyasa da ake nunawa a kasar zai yi farautar PDP a cikin shekaru masu zuwa.”
Da yake karbar wadanda suka sauya shekar zuwa jam’iyyar APC a ranar Lahadi, 6 ga watan Fabrairu, Kwamishinan Hukumar Kidaya ta Kasa, Cif Richard Odibo ya nuna farin cikinsa da sauya shekar da Shugaban Jam’iyyar PDP na garin Egini ya yi.
Ya kuma jaddada cewa zai tabbatar da sabbin mambobin sun samu hakinsu a APC.
Siyasar Kano: An yi zaman sulhu tsakanin bangaren Ganduje da Shekarau, an cimma matsaya
A wani labarin kuma, mun ji cewa kwamitin riko na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa karkashin jagorancin Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe ya cimma matsaya a kan rikicin cikin gida da ya dabaibaye jam’iyyar reshen Kano.
Sashin Hausa na BBC ya ruwaito cewa a ranar Asabar, 5 ga watan Fabrairu, kwamitin ya kira taron gaggawa tsakanin bangarorin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da Sanata Ibrahim Shekarau.
Hakan ya biyo bayan tattara bayanai da kwamitin ya yi a ranar Talata, 25 ga watan Janairu.
Asali: Legit.ng