Shugaban kasa a Twitter: Dan Elrufa'i ya yiwa mai neman takara a 2023 ba'a
- Yaron gwamnan jihar Kaduna, Bashir El-Rufai, ya yi ba'a ga masu neman takarar shugaban kasa a 2023 ba'a
- Bashir ya bayyana cewa Peter Obi ba zai kai labari ba inda ya ce shi kuma Kingsley Moghalu shugaban kasar Najeriya ne amma na Twitter
- Dama dai matashin ya yi kaurin suna wajen yiwa wadanda yake adawa da su shagube a shafin Twitter
Dan gwamnan jihar Kaduna, Bashir Nasir El-rufai ya je shafinsa na Twitter domin yiwa Peter Obi da Kingsley Moghalu ba’a.
Peter Obi ya kasance dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a zaben 2019 kuma mai neman takarar shugaban kasa a zaben 2023 mai zuwa.
Dan gwamanan Kadunan ya yi shagube ga kudirin takarar shugabancin tsohon gwamnan na jihar Anambra, Obi da tsohon mataimakin babban bankin Najeriya, Moghalu.
Bashir, wanda ya yi kaurin suna wajen yin sharhin tsokana a Twitter ya yi wallafa inda ya yi hasashen cewa Obi ba zai iya lashe zaben shugaban kasar ba, yayin da yace Moghalu shugaban kasar Najeriya reshen Twitter ne.
Ya ce:
“Peter Obi ba zai iya lashe zabe ba. Kingsley Moghalu shi shugaban kasar Najeriya (reshen Twitter) ne dan Allah.”
Obi dai ya bayyana cewa zai yi takara idan jam’iyyarsa ta PDP ta mika tikitinsa zuwa kudu.
A daya bangaren, Moghalu wanda ya kasance dan takarar shugaban kasa na kam Young Progressive Party (YPP) a 2019, ya ce zai sake yin takara a zaben shugaban kasa na 2023.
Dan Allah kada ku maida matasa yan daban zaɓe, Tsohon Shugaba ya roki yan siyasa
A gefe guda, mun ji cewa tsohon shugaban Najeriya, Janar Abdulsalami Abubakar, ya gargaɗi yan siyasa kada su maida matasa yan daba masu tada rikicin siyasa, waɗan da zasu yi amfani da su a zaɓe mai zuwa.
Jaridar Punch ta rahoto tsohon shugaban ƙasa na cewa damuwar tsaron da ƙasar nan ke ciki kaɗai ya ishe ta tagumi.
Abdulsalami ya yi wannan gargaɗin ne yayin da ya karɓi Digiri na uku a wurin taron yaye ɗalibai kashi na 30 na jami'ar Fasaha ta tarayya, Minna ranar Laraba.
Asali: Legit.ng