Dan Allah kada ku maida matasa yan daban zaɓe, Tsohon Shugaba ya roki yan siyasa
- Janar Abdulsalami Abubakar mai ritaya ya gargaɗi yan siyasan Najeriya kada su yi amfani da matasa a matsayin yan daban siyasa
- Tsohon shugaban ƙasa ya kuma shawarci matasa su yi amfani da wayewarsu, kada su bar wani ya yi amfani da su
- Ya bayyana matsalar tsaron da ƙasa ke fama da shi a matsayin wani yaƙi mara tushe, ana kashe mutane babu dalili
Minna - Tsohon shugaban Najeriya, Janar Abdulsalami Abubakar, ya gargaɗi yan siyasa kada su maida matasa yan daba masu tada rikicin siyasa, waɗan da zasu yi amfani da su a zaɓe mai zuwa.
Jaridar Punch ta rahoto tsohon shugaban ƙasa na cewa damuwar tsaron da ƙasar nan ke ciki kaɗai ya ishe ta tagumi.
Abdulsalami ya yi wannan gargaɗin ne yayin da ya karɓi Digiri na uku a wurin taron yaye ɗalibai kashi na 30 na jami'ar Fasaha ta tarayya, Minna ranar Laraba.
Ya kuma shawarci matasa kada su bari wani ɗan siyasa ya yi amfani da su wajen tada yamutsi.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Yace:
"Yayin da gangar siyasa ta kaɗa, ina gargaɗin yan Najeriya da yan siyasa su buga wasan da basira. Kada ku yi amfani da yaran mu da jikokin mu wajen yaɗa Farfaganda da zage-zage, wanda kun san ba dai-dai bane."
"Gare ku matasan mu, ku guji bari a yi amfani da ku a matsayin yan daban siyasa waɗan da za su tada zaune tsaye, su hana zaman lafiya."
Halin rashin tsaro a Najeriya
Tsohon shugaban ya bayyana rashin tsaron da ƙasa ke fama da shi da wani yaƙi da babu hankali cikinsa, inda ake kashe mutane ba tare da dalili ba.
"Muna fuskantar matsanancin lokaci na rashin tsaro wanda ya shafi ko ina, mahaukacin yaƙi, wanda ake kashe tsoho da yaro ba tare da dalili ba."
"Komai ya koma kan jami'an tsaron mu, yanzun ya rage namu, mu haɗa hannu wajen fallasa bayanan da ya dace domin shawo kan matsalar."
A wani labarin na daban kuma Sule Lamiɗo yace ba wanda ya isa ya kai tikitin takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar PDP wani yanki
Jigon jam'iyyar hamayya PDP, Sule Lamiɗo,ya yi fatali da batun tsarin mulkin karba-karba yayin fitar da ɗan takara.
Tsohon gwamnan jihar Jigawa ya ce Najeriya na bukatar nagartaccen jagora wanda jama'a suke kauna.
Asali: Legit.ng