Mutanen Twitter sun ba PDP shawarar ta tsaida Peter Obi/Kwankwaso a zaben 2023
- Yayin da zaben 2023 ya gabato, mutane su na ta bayyana wanda suke sha’awar ya nemi shugabanci
- Wasu sun fito shafin Twitter su na bada shawarar a tsaida Rabiu Musa Kwankwaso da Peter Obi a PDP
- Masu wannan tunani su na ganin hakan zai taimakawa jam’iyyar PDP wajen doke APC a zabe mai zuwa
A wannan rahoto, Legit.ng Hausa ta bibiya abin da mutane suke fada a shafin sada zumunta na Twitter a ranar Laraba, 2 ga watan Fubrairu 2022.
Kevin Odanz ya jawo gardama da ya ce Peter Obi ba zai kai labari idan ya nemi tikitin PDP ba, ya ce ko zai yi nasara, 'Yan Arewa ba za su zabe shi ba.
Tuni wasu suka shiga maida masa martani, su na cewa tsohon gwamnan na Anambra ne zai iya doke APC, musamman idan ya tafi da Kwankwaso
Wani Otumba ya ce ya fahimci siyasar Najeriya, ya gano cin zabe sai an hada da yankin Arewa, ya na ganin Kwankwaso zai taimaka wajen doke APC.
Tweet Judon ya yi kira ga Peter Obi ya juyawa Atiku Abubakar baya a zabe mai zuwa na 2023.
“@PeterObi, ka yi kokari ka tuntubi Saraki ko Kwankwaso. Ka bar mana sauran aikin mu magoya baya. Najeriya ta na bukatarka, ka da ka ba mu kunya.”
“Babu laifi don ka yi fatali da Atiku, ‘Dan Adam ne shi wanda ya gaza sau da yawa. Ka sha gabansa.”
- Tweet Judon
Ana neman mai kishin Arewa
Wata Baiwar Allah mai suna NEFERTITI ta ce za ta so ta ga Peter Obi da Kwankwaso a tikiti, inda ta tuna da Dadiyata da aka dauke tun a shekarar 2019.
“Kwankwaso ya na da matukar farin jini a Arewacin Najeriya, babu wanda ya isa ya raina tafiyar jar hula ta Kwankwasiyya.”
- @firstladyship
“Daya daga cikin El-Rufai ko Kwankwaso yana bukatar ya zama Mataimakin shugaban kasa a Najeriya. Ina bukatar shugabannin da suka damu da Arewa.”
- A cewar Sani Waspapping
"Tsaida Peter Obi da Kwankwaso ba shirme ba ne."
- Chris Blin
“Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya na da magoya baya ‘yan a – mutu. Idan jam’iyyar PDP ta na so ta yi nasara a zaben 2023, ta ba shi takara, ba za tayi nadama ba.”
- Kwankwasiyya Frontiline
“Ni ma zan so in ga Peter Obi/ Kwankwaso a filin zabe. Wadannan jagorori biyu sun yi kokari a lokacin da suka yi mulkin jihohinsu.”
- Inji The Real Girl
Kwankwaso kadai zai kai labari
"Tikitin Obi da Tambuwal ba zai kai ko ina ba. Amma Obi/Kwankwaso zai karbu a Zaria-Zurich, Sapele-Singapore ko tun daga Potaskum zuwa Poland."
2023: Malaman addinin Musulunci da Kirista fiye 1,000 sun yi taron yi wa gwamnan APC addu’o’in samun nasara
- PDP vanguard
"Za a iya tallata takarar Obi/Kwankwaso."
- PDP vanguard
"A ra’ayina, ‘yan takarar da suka fi karfi daga kabilu uku da ake da su, su ne Peter Obi, Rabiu Kwankwaso da kuma Gwamna Seyi Makinde."
Sun san darajar ilmi
Shi kuma wani cewa ya yi, da Kwankwaso da Obi duk sun yi tarayya wajen son ilmi, ya ce za a gyara harkar ilmi idan wadannan biyu suka samu shugabanci.
"Wadannan mutane sun san darajar ilmi, kuma aka yi dace dukkaninsu sun fito ne daga jam’iyya guda. Amma ko meyasa PDP ta ke kaunar Atiku?
- Prince Charles
"A ba Peter Obi, Kwankwaso a matsayin abokin takararsa, duk wadannan maganar kuri’un Arewa za su zama labari … Idan PDP da gaske ta ke yi, Peter Obi da Kwankwaso za su canza masu lissafi.”
- Ikukoma C
"Peter Obi/Kwankwaso madalla ne #2023Elections #PeterObi4President"
- A ra'ayin Oyibo Chijioke
Kwankwaso ya yi shiru
Dazu kun ji ‘yan siyasa da-dama su na ta bayyana manufarsu ta tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2023, amma har yanzu Rabiu Kwankwaso bai ce komai ba.
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar, Nyesom Wike, da irinsu Rabiu Kwankwaso ba su fito a mutum, sun bayyanawa Duniya nufinsu ba.
Asali: Legit.ng