Ka rike girman ka: Tsohon Minista ya ja-kunnen Shugaba Jonathan a kan kwadayin mulki
- Solomon Ewuga ya ba Goodluck Jonathan shawara ya yi watsi da masu ce masa ya sake takara
- Sanata Ewuga ya na ganin mutuncin Jonathan zai zube a idanun Duniya idan ya kuma neman mulki
- Tsohon Ministan ya tabbatar da cewa zai tsaya takarar gwamna a jihar Nasarawa a zabe mai zuwa
Abuja - A karshen makon jiya aka ji cewa Sanata Solomon Ewuga ya yi kira ga Goodluck Jonathan ya yi watsi da masu neman ya kuma takara a Najeriya.
Jaridar Vanguard ta rahoto Solomon Ewuga yana cewa fitowa neman kujerar shugaban kasa a 2023 zai batawa Goodluck Jonathan suna da kimarsa ne kurum.
Da yake magana da manema labarai a garin Abuja, Ewuga ya ce idan Jonathan ya biyewa masu wannan kira, darajarsa da ake gani a duk fadin Duniya zai fadi.
A ra’ayin tsohon ‘dan majalisar, bai kamata Jonathan ya jefar da kallon mutuncin da ake yi masa ba.
A hirar da ya yi, Sanata Ewuga ya kuma ba jam’iyyar hamayya ta PDP shawara ta gyara duk wasu kura-kuran da tayi a baya, idan ta na so al’umma su sake zabenta.
“Idan ka tambaye ni, martaba da kimar da Jonathan ya samu da ya sallama kujerar shugaban kasa a 2025 ta fi karfin ayi watsi da shi saboda neman takara.”
“Masu kiran Jonathan ya dawo Aso Villa su ne wadanda suka bata masa suna a zaben 2015.” - Solomon Ewuga
APC ta sa mutane a wahala
The Street Journal ta ce Ewuga wanda ya taba rike kujerar Ministan babban birnin tarayya Abuja ya koka a game da irin wahalar da mutanen kasar suke sha a yau.
2023: Malaman addinin Musulunci da Kirista fiye 1,000 sun yi taron yi wa gwamnan APC addu’o’in samun nasara
Sanata Ewuga ya zargi shugabanni da jefa jama’a a cikin wannan mawuyacin hali inda ya yi kira da ‘Yan Najeriya su guji siyasar son-kai, su zabi nagari a zaben 2023.
Bayan kiran ayi amfani da wannan dama ayi waje da gwamnatin APC a zabe mai zuwa, Solomon Ewuga ya tabbatar da cewa zai tsaya takarar gwamnan Nasarawa.
Clark zai iya yin Saraki a 2023
An ji tsohon Ministan sadarwa tun a mulkin Janar Yakubu Gowon, Cif Edwin Clark mai shekara 94 ya karbi maganar takarar Bukola Saraki da hannu biyu-biyu.
A halin yanzu tsohon shugaban majalisar dattawa, Saraki ya fara yakin neman tikiti, kuma Clark ya nuna zai iya mara masa baya idan 'Dan kudu bai samu tikiti ba.
Asali: Legit.ng