1992, 2007, 2011, 2015 da 2019: Tarihin takarar Shugaban kasa 6 da Atiku Abubakar ya yi

1992, 2007, 2011, 2015 da 2019: Tarihin takarar Shugaban kasa 6 da Atiku Abubakar ya yi

  • Atiku Abubakar ya saba fitowa takarar shugaban kasa a Najeriya tun a lokacin sojoji su na mulki
  • Ana kyautata zaton tsohon mataimakin shugaban kasar zai iya sake fitowa takaran a zaben 2023
  • Idan Atiku ya tsaya takara a 2023, zai kasance ya nemi kujerar shugaban kasa sau shida a tarihi

Yayin da aka fara kada gangunan siyasa a Najeriya, wasu sun fara hasashen cewa Wazirin Adamawa, Alhaji Atiku Abubakar zai sake neman takara.

Mun tattaro lokutan da Atiku Abubakar ya nemi kujerar shugaban kasar Najeriya a babban zabe ko zaben fitar da gwani, ko akalla ya yi niyyar neman mulki.

1. Zaben 1999

Atiku Abubakar ya nemi ya tsaya takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar SDP a zaben 1999 bayan an haramtawa su Janar Shehu Musa ‘Yar’adua shiga siyasa.

Kara karanta wannan

Kungiyar Inyamurai ta Ohanaeze: Ba mu amince da shawarar Atiku ta yin wa'adi daya a mulkin Najeriya ba

Irinsu Shehu ‘Yar’adua sun marawa Atiku baya a zaben tsaida ‘dan takara da aka shirya a Jos, amma sai ya zo na uku a bayan MKO Abiola da Babagina Kingibe.

2. Zaben 2003

Ana tunanin cewa Atiku Abubakar ya yi yunkurin neman tikitin jam’iyyar PDP a zaben 2003, amma mai gidansa a lokacin, Olusegun Obasanjo ya shawo kansa.

Bayan shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya samu tazarce, sabani ya shiga tsakaninsa da Atiku.

3. Zaben 2007

A karshe dole Atiku Abubakar ya fice daga jam’iyyar PDP a dalilin rigimarsa da shugaba Obasanjo, ya shiga ACN kuma ya samu tikitin takarar shugaban kasa.

Atiku Abubakar
Atiku Abubakar a Kano a 2019 Hoto: www.channelstv.com
Asali: UGC

A babban zaben 2007 Atiku ya zo na uku ne bayan Ummaru ‘Yar’adua da Muhammadu Buhari.

4. Zaben 2011

A zaben da aka yi a shekarar 2011 ba a bar Atiku Abubakar a baya ba. Babban ‘dan siyasar ya gwabza da shugaba mai-ci Goodluck Jonathan wajen samun tikitin PDP.

Kara karanta wannan

Tun bayan zaben 2019 Atiku ya gudu Dubai, sai yanzu ya dawo lokacin da zabe ya gabato: Jigon PDP

A karshe dai Goodluck Jonathan ya lashe zaben fitar da gwanin da jam’iyyar PDP ta shirya, kuma ya yi nasara a babban zabe inda ya doke irinsu jam’iyyun CPC da ACN.

5. Zaben 2015

Daga baya Atiku ya sake barin PDP a wani karon, ya shiga sabuwar jam’iyyar APC da aka kafa da nufin ya yi takarar kujerar shugaban kasa a zaben 2015, amma bai dace ba,

A zaben tsaida ‘dan takara da jam’iyyar APC ta shirya a Legas a Disamban 2014, Atiku Abubakar ya zo na uku ne – bayan Muhammadu Buhari da Rabiu Musa Kwankwaso.

6. Zaben 2019

Har ila yau Atiku Abubakar bai hakura a 2019 ba, da shi aka nemi tutar PDP a garin Fatakwal inda ya doke su Aminu Tambuwal, Bukola Saraki da Kwankwaso, da sauransu.

A babban zaben da aka shirya, Atiku da jam’iyyar PDP sun sha kashi a hannun Muhammadu Buhari na APC mai mulki. An ba PDP ratar kuri'u fiye da miliyan uku a zaben.

Kara karanta wannan

Duk da ya jarraba sa’a sau 3 babu nasara, Sanatan APC zai sake neman Shugaban kasa

Tinubu a 2023

Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu ya sha alwashin za su ba Bola Tinubu gudumuwar mutane 1500 domin ya karbi mulkin Najeriya a zabe mai zuwa da za ayi a 2023.

A jiya aka ji Sanwo-Olu da wasu magoya baya sun kafa tafiyar Asiwaju Bola Ahmed Tinubu Movement.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng