Gwamnan APC ya yi alkawarin ba Bola Tinubu mutum 1500 da za su taya shi yakin zabe
- Gwamnan jihar Legas yana tare da tsohon mai gidansa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a zabe mai zuwa
- Babajide Sanwo-Olu da wasu magoya baya sun kafa tafiyar Asiwaju Bola Ahmed Tinubu Movement
- Wannan kungiya ta na kokarin ganin ta tara mabiya akalla 1, 500 da za su taya Tinubu yakin neman zabe
Abuja - Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu ya ce dabarar da ta fi kowace ita ce a bar Asiwaju Bola Tinubu ya karbi shugabancin kasar nan a 2023.
Jaridar Punch ta ce Babajide Sanwo-Olu ya yi wannan bayani wajen rantsar da shugabannin tafiyar Asiwaju Bola Ahmed Tinubu Movement a Ikeja, jihar Legas.
Sanwo-Olu ya ce za su kawo mutane sama da 1, 500 da za su dage wajen ganin tsohon gwamna Bola Tinubu ya yi nasarar zama shugaban kasa a shekarar badi.
Gwamna Sanwo-Olu ya fadi irin mutumin da ake bukata ya karbi ragamar shugabancin kasar nan a zabe mai zuwa, ya ce wannan ba kowa ba ne sai shi Tinubu.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Jawabin Babajide Sanwo-Olu
“Mun taru a nan ne domin a samar da sojoji, jagorori, abokan tafiya da ‘yan kanzagi fiye da 1500 daga kananan hukumomi da LCDAs 57 da mazabunmu 377 a fadin duk wani lungu da kwararo na jihar Legas.”
“Mu fita mu karfafawa mutanenmu baya a kan wanda za a zaba ya gaji Muhammadu Buhari, wanda zai iya cigaba daga inda ya tsaya a mulki a shekara mai zuwa, ya yi aikin da ake bukatar fito da Najeriya.”
“Dole wannan mutumi ya zama maras kabilanci, wanda ya san jama’a a ko ina a fadin kasar nan, kuma ya yi imani da hadin-kan mutanenmu da ganin yiwuwar shawo kan duk wasu kalubale da za a fuskanta.”
“Ya zama dole ya zama wanda ya san damukaradiyya, ya yi imani da tsarin tarayya, sannan kuma ya zama wanda aka yarda da shi ya jagoranci mutane, kuma wannan mutumi shi ne Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.”
“Shi ne zabin da bai kamata ya kubucewa Najeriya a zaben 2023 ba.” – Sanwo-Olu.
Mudashiru Obasa ya na layin Tinubu
Mudashiru Obasa ya halarci wannan taro na kaddamar da ABAT. Shugaban majalisar dokokin na jihar Legas ya ce ABAT sabuwar tafiya ce da za ta tallata Bola Tinubu.
Tinubu ya yi digiri
Dazu aka ji cewa wani babban jami’in jami’ar jihar Chicago, Beverly Poindexter ya tabatar da Bola Tinubu ya yi digiri a makarantarsu, akasin jita-jitar da ake yadawa.
A shekarar 1999 an taba kai kara a kotu, ana neman a hukunta Bola Tinubu saboda zargin cewa yana karyar ya yi karatun jami’a, tun lokacin ake ta kai ruwa rana.
Asali: Legit.ng