Yanzu-yanzu: Biodun Oyebanji ya lashe zaben fiddan gwanin dan takaran APC a jihar Ekiti

Yanzu-yanzu: Biodun Oyebanji ya lashe zaben fiddan gwanin dan takaran APC a jihar Ekiti

  • Bayan sa'o'i ana fafatawa, an sanar da sakamakon zaben fiddan gwanin dan takaran jam'iyyar APC a Ekiti
  • Alkalin zaben ya sanar da cewa Biodun Oyebanji ne ya samu rinjaye a zaben da ya gudana ranar Alhamis
  • Yanzu Biodun Oyebanji zai kara da dan takaran jam'iyyar PDP, Bisi Kolawale a zaben gwamnan jihar Ekiti

Tsohon Sakataren gwamnatin jihar Ekiti, Biodun Oyebanji, ya kayar da sauran yan takara bakwai a zaben fiddan gwanin dan takaran gwamnan jihar Ekiti karkashin inuwar jam'iyyar APC.

Biodun Oyebanji ya lallasa abokan takaransa da tazara sama da 100,000., rahoton TVC.

Yayinda ya samu kuri'u 101,703, wadanda ke biye da shi ya samu kuri'u 767.

Alkalin Zaben, Gwamnan jihar Jigawa, Muhammad Badaru, ya sanar da sakamakon.

Yanzu-yanzu: Biodun Oyebanji ya lashe zaben fiddan gwanin dan takaran APC a jihar Ekiti
Yanzu-yanzu: Biodun Oyebanji ya lashe zaben fiddan gwanin dan takaran APC a jihar Ekiti
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Da duminsa: Yan takara 7 a zaben fidda gwanin APC sun janye, sunce Gwamnan murdiya ya shirya

Ga jerin sakamakon:

1. Bamidele Faparusi - 376

2. Ojo Kayode - 767

3. Opeyemi Bamidele - 760

4. Dayo Adeyeye - 691

5. Femi Bamisile - 400

6. Oyebanji Abiodun - 101,703

7. Toyin Afolabi - 47

8. Demola Popoola - 239

Yan takara 7 a zaben fidda gwanin APC sun janye, sunce Gwamnan murdiya ya shirya

Mun kawo muku cewa yan takaran kujeran gwamnan jihar Ekiti guda bakwai sun janye daga zaben fidda gwanin da jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta shirya yau a jihar.

Yan takaran sune; Kayode Mojo, Demola Popoola, Femi Bamisile, Bamidele Faparusi, Dayo Adeyeye, Opeyemi Bamidele da Afolabi Oluwasola.

Sun yi zargin cewa kwamitin zabe cike take da yaran Gwamnan jihar, Kayode Fayemi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng