Dan majalisa daga Gombe ya lissafo gwanayensa, ya ce daya daga cikinsu ne ya cancanci ya gaji Buhari

Dan majalisa daga Gombe ya lissafo gwanayensa, ya ce daya daga cikinsu ne ya cancanci ya gaji Buhari

  • Dan majalisar tarayya daga jihar Gombe, Hon Simon Karu, ya bayyana gwanayensa da ya kamata APC ta bai wa tikitin takarar shugaban kasa a zaben 2023
  • Karu ya ce daya daga cikin Yemi Osinbajo, Babatunde Fashola da Femi Gbajabiamila ya cancanci ya maye gurbin Buhari a zabe mai zuwa
  • Ya ce wadannan manyan yan siyasa uku suna da abun da ake bukata a wajen wanda zai zama shugaban kasa

Gombe - Dan majalisar wakilai mai wakiltan mazabar Kaltungo/Shongom na Gombe, Hon Simon Karu, ya bayyana yan takarar da suka cancanci su gaji shugaban kasa Muhammadu Buhari a zaben 2023.

A cewar Karu, mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, ministan ayyuka da gidaje, Babatunde Raji Fashola ko Femi Gbajabiamiala ne suka cancanci samun tikitin takarar shugaban kasa na jam'iyyar All Progressives Congress (APC).

Kara karanta wannan

Iyayen mutumin da ya kashe Hanifa sun gudu daga gidansu saboda tsoron hari

Dan majalisa daga Gombe ya lissafo gwanayensa, ya ce daya daga cikinsu ne cancanci su gaji Buhari
Dan majalisa daga Gombe ya lissafo gwanayensa, ya ce daya daga cikinsu ne cancanci su gaji Buhari Hoto: Punch.com
Asali: UGC

A wata hira da aka yi da shi, dan majalisar ya ce kowanne daga cikinsu zai kai kasar ga matakin ci gaba idan har aka mika mulki ga yankin kudu, The New Telegraph ta rahoto.

Karu ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Idan aka mika mulki yankin kudu, ta yiwu kudu maso yamma saboda yawan mabiyanta a jam'iyyar mai mulki.
"Ina ganin akwai manyan mutane uku da suka cancanci shiga wannan tseren ko shakka babu da tarin kwarewa. Farfesa Yemi Osinbajo, Fashola da kakakin majalisar wakilai Gbajabiamila sun cancanta.
“Wadannan mutanen suna da kyawawan halaye a matsayinsu na manyan yan kasa sannan suna da kwazo.
"Ko shakka bana yi cewa wadannan mutane uku suna da abun da ake bukata da karfin nasara a kowani zaben kasa kuma za su nuna bajinta."

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa da aka tambaye shi kan kudirin takarar shugabancin babban jagoran jam'iyyar All Progressives Congress (APC) Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Karu ya ce:

Kara karanta wannan

Atiku shekaru 4 kadai zai yi idan ya hau mulki, Shugaban kwamitin yakin zabensa

"To, Tinubu ya yi zamaninsa kuma babu shakka ya kasance jarumi a kudu, amma lokaci da yanayi yana da mahimmanci ga kowane jarumi "zamani goma (10) sarki goma (10)" wannan yana nufin kowane sarki da lokacinsa. Tinubu ba sarki ba ne kuma masu nada sarki ba su da hurumin zama sarakuna.”

Ba gaskiya bane: Miyetti Allah ta yi watsi da batun goyon bayan Tinubu a zaben 2023

A gefe guda, kungiyar Miyatti Allah ta Najeriya (MACBAN), ta ce bata goyon bayan kudirin takarar shugabancin kowani dan takara a babban zaben 2023.

Babban sakataren MACBAN, Alhaji Baba Ngelzarma, ya bayyana hakan a wata sanarwa ga manema labarai a ranar Laraba, 25 ga watan Janairu, a Abuja, PM News ta rahoto.

Ngelzarma ya ce kungiyar tana mutunta takarar dukkanin yan takarar shugaban kasa sannan cewa lokaci bai yi da za ta fitar da wanda zata marawa baya ba, rahoton Daily Post.

Kara karanta wannan

Tanko Yakasai: 'Yan Arewa ba sa tsinana komai a Najeriya, a ba 'yan kudu mulki a 2023

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng