Takarar Shugaban kasa: Fito-na-fito da Tinubu, da kalubale 4 da suke jiran Osinbajo a 2023

Takarar Shugaban kasa: Fito-na-fito da Tinubu, da kalubale 4 da suke jiran Osinbajo a 2023

  • Ba abin mamaki ba ne don mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo ya nemi shugabanci a 2023
  • Akwai wasu kalubale da Farfesa Yemi Osinbajo zai iya fuskanta idan ya fito takara a zaben 2023
  • Daga ciki shi ne zai yi takara da Ubangidansa, Bola Tinubu wanda ya yi sanadiyyar zamansa wani

Abuja - Ana ganin mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo yana cikin wadanda za a iya gwabzawa da su wajen nemen tikitin APC da babban zaben 2023.

Har yanzu Farfesa Yemi Osinbajo bai bayyana niyyarsa na tsayawa takarar shugaban kasa ba. Amma akwai mutane da-dama da suke kiransa ya nemi mulkin.

Daily Trust ta kawo wasu abubuwa da za su iya zama cikas ga Yemi Osinbajo idan ya fito takara. A cikin masu goyon-bayan sa har da gwamnoni da Sarakunan Arewa.

Kara karanta wannan

Tseren shugabancin APC ya koma tsakanin Sanatoci 2, da tsohon Ministan Buhari

Gwamnonin biyu sun fito ne daga Arewa maso yamma, biyu kuma su na yankin Arewa ta tsakiya.

Wasu cikas Farfesan zai iya fuskanta a zabe mai zuwa?

1. Karo da Jagaban

Babbar matsalar da ke gaban Yemi Osinbajo ita ce burin Bola Tinubu wanda shi ya yi masa riga da wando a siyasa tun daga 1999 har zuwa zaben 2015.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Tinubu ya dauko Osinbajo a matsayin Kwamishinan shari’a a lokacin ya na gwamna. A sanadiyyarsa ne kuma Farfesan ya zama ‘dan takarar APC.

Har gobe Tinubu ne yake da ta-cewa a APC a Legas – inda Osinbajo ya fito. Idan mataimakin shugaban kasar ya nemi tikiti, zai gamu da cikas daga gida.

Shugaban kasa
Muhammadu Buhari da Yemi Osinbajo Hoto: BBCNewsHausa
Asali: Facebook

2. Fasto a cocin RCCG

Duk da cewa Yemi Osinbajo Farfesa ne kuma babban lauya na kasa, shi din Fasto ne wanda ya kai matsayin Limami a reshen cocin RCCG mai dinbin mabiya.

Kara karanta wannan

Osinbajo ya bada labarin yadda ya zama Mataimakin Buhari lokacin ba a san shi ba

Watakila wasu musulmai musamman daga yankin Arewa za su fi sha’awar ganin ‘dan siyasa wanda akidarsa da ra’ayin addini ba su bayyana ba, ya karbi mulki.

3. Masu rike da madafan iko

Rahoton ya ce kafin Osinbajo ya iya zama shugaban Najeriya, yana bukatar goyon bayan mai gidansa, Muhammadu Buhari da boyayyun masu rike da madafan iko.

A lokacin da Osinbajo ya samu damar rikon kwarya, ya dauki matakan da ake ganin ya taka masu juya akalar mulki, yana bukatar sa hannun wadannan mutane a 2023.

4. Laifin APC

Ga masu ganin jam’iyyar APC ta ba mutane kunya ko kuma suke jin haushin gwamnatin Muhammadu Buhari, Yemi Osinbajo ma yana cikin matsalolin kasar.

Irin wadannan mutanen za su yi kokarin ganin hakar Osinbajo ba ta cin ma ruwa ba, idan ya fito ya na neman a zabe shi domin APC ta cigaba da shugabancin kasa.

5. Kwarewa a siyasa

Masu hasashe su na ganin Farfesa Osinbajo ba cikakken ‘dan siyasa ba ne domin bai da ta-cewa a tafiyar APC don haka sai ya yi da gaske kafin ya iya samun nasara a zabe.

Kara karanta wannan

2023: Ganduje, da jerin ‘Yan siyasa 10 a yankin Arewa da za su karfafi takarar Bola Tinubu

Siyasar PDP

Kun ji cewa gwamnan Ribas, Nyesom Wike zai jikawa jagororin jam’iyyar PDP na Arewacin Najeriya aiki wajen neman tikitin tsayawa takarar shugaban kasa a 2023.

Gwamnan ya fara neman hadin-kan wasu Gwamnoni 5 da za su taimaka masa wajen cin ma nufinsa na hana PDP ta kai takarar shugaban kasa zuwa Arewacin kasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng