Aisha Buhari ga APC: Mun gaji da gafara Sa, ku bai wa mata manyan mukamai

Aisha Buhari ga APC: Mun gaji da gafara Sa, ku bai wa mata manyan mukamai

  • Uwargidan shugaban kasa, Aisha Buhari ta bukaci jam’iyyar APC ta tabbatar mata sun samu mukamai masu tsoka a cikin ta
  • A ranar Talata yayin wani taron mata ‘yan jam’iyyar da aka yi a Abuja, ta bayyana wannan bukatar inda tace hakan zai kawo ci gaba
  • Aisha Buhari ta ce hakan ce babbar mafita wacce za ta bunkasa mata a siyasance da tattalin arzikin kuma ta ba su kaimi wurin shiga siyasa

FCT, Abuja - Uwargidan shugaban kasa Muhammadu Buhari, Aisha Buhari ta bukaci jam’iyyar APC da ta dinga bai wa mata mukamai masu tsoka a cikin jam'iyyar.

Aisha ta yi wannan furucin ne a ranar Talata a wani taron mata na jam’iyyar APC ta kasa da aka yi a Abuja, TheCable ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Mijina yana cizo na, ya lakaɗa mun duka idan ban yi abinci ba, Mata ta nemi kotu ta raba auren

Aisha Buhari ga APC: Mun gaji da gafara Sa, ku bai wa mata manyan mukamai
Aisha Buhari ga APC: Mun gaji da gafara Sa, ku bai wa mata manyan mukamai. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ta kara da cewa alhakin ci gaban Najeriya ya rataya a wuyan mata ne inda tace ya kamata APC ta daina furta shigar da mata cikin gwamnati, ta dinga sanya su gaba-gadi.

Kamar yadda tace:

“Wannan ne taron matan APC na kasa na farko da aka shirya don saita mata a mukamai na gwamnatin tarayya, musamman don tabbatar da mata su na rike mukamai na siyasa da kuma kara musu kwarin guiwa wurin samar da ci gaba ga jam’iyyar mu mai girma,” a cewar ta.
“Tun 2015, na samu damar shigar da matan Najeriya cikin harkoki daban-daban. Na jajirce ne don ganin alhakin kasar nan ya rataya a wuyan matan mu.
“Kuma hakan ya na sa jam’iyyar mu ta kara bunkasa kuma mata da dama sun sanya hannu wurin ci gaban kasar nan.

Kara karanta wannan

Rashin Imani: Mahaifiya ta wanke ɗiyar cikinta da tafasasshen ruwa kan aike

“Hakan yasa na ke kira ga APC da ta nunka kokarin ta wurin ciyar da mata gaba wanda na yarda zai taimaka wurin tabbatar da wannan makasudin namu.
“Yayin da ake shirin yin wani zabe a Najeriya, wajibi ne mu daina furtawa sai dai aiwatarwa. Mu sanya mata a mukamai manya na jam’iyya da gwamnati.
“Wajibi ne mu tabbatar hakan ya auku; don daga wurin mu za a yi koyi. Sai APC ta fara tabbatar da ta nada mata a mukamai masu kyau a jam’iyyar kafin a kai ga na gwamnati.
“Idan hakan ta faru, bunkasa matan Najeriya zai zama abu mai sauki wurin tunkarar mukaman siyasa da na tattalin arziki.”

A cewarta, tabbatar da shigar mata siyasa zai taimaka wurin ciyar da kasar nan gaba. Kuma alamu suna nuna cewa jam’iyyar APC za ta ci gaba da samun nasarori.

“An dade ana dakusar da mata da dama amma yanzu an fara jin muryoyin su kuma za su haska cikin al’umma nan ba da jimawa ba,” a cewarta.

Kara karanta wannan

Shugaban kasa a 2023: Shugaban PDP ya yi magana kan magajin Buhari

Ta ce akwai bukatar a sanya mata ofisoshi na zartar da hukunci tun daga kananun hukumomi, jihohi da kuma matakan gwamnatin tarayya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng