Sanatocin jihar Katsina 2 sun shafe watanni 25 a Abuja, ba su kawo korafi ko shawara 1 ba

Sanatocin jihar Katsina 2 sun shafe watanni 25 a Abuja, ba su kawo korafi ko shawara 1 ba

  • Daga cikin aikin ‘Yan majalisa shi ne su bada shawara domin gwamnati ta dauki matakin da ya kamata
  • Sannan kuma ‘Yan majalisa su kan kawo korafin mutanen mazabarsu domin a share masu hawaye
  • Sanatocin kudu da Arewacin Katsina sun shafe shekaru biyu a mulki ba tare da wata gudumuwa ba

Abuja - Daga lokaci zuwa lokaci, a kan bibiyi abubuwan da masu mulki suka yi tun daga lokacin da suka shiga ofis. Wannan sanannen abu ne a harkar siyasa.

Jaridar Order Paper ta yi bincike a game da irin kokarin da ‘yan majalisa suke tabukawa, inda ta gano babu wata gudumuwa da Sanatocin Katsina su ka bada.

A wannan majalisa da aka rantsar Yunin 2019, an samu Sanatocin da suka fito daga Katsina da ba su bada gudumuwar kudiri ko korafi ba har zuwa Mayun 2021.

Kara karanta wannan

Kaduna: 'Yan ta'adda sun bude wa 'yan biki wuta, sun halaka 4, wasu sun jigata

Sanata Kabiru Abullahi Barkiya mai wakiltar Katsina ta tsakiya shi ne ya yi kokari, har ya gabatar da wasu gudumuwa biyu da korafi daya a kusan shekaru uku.

Order Paper ta ce Sanata Barkiya ya yi magana ne a kan halin rashin tsaro da ake fuskanta a mazabarsa, ya yi kira ga hukumar NEMA ta kai wa yankin agaji.

Bayan nan kuma an taba jin Kabiru Abullahi Barkiya yana bada shawarar farfado da masana’antun gida ta hanyar taimaka masu da bashin bankin BOI.

Sanatocin jihar Katsina
Sanatocin jihar Katsina Hoto: Order Paper
Asali: UGC

Har ila yau, Sanatan ya na da korafi guda a kan kamfanonin sadarwa da suka sa karafunansu a Abuja. Wannan ne kadai korafin da ya kai majalisar dattawan.

A gefe guda kuwa, babu wata shawara ko korafi da ta fito daga bakin Sanatan Katsina ta Arewa, Ahmad Babba Kaita tun daga lokacin da aka sake rantsar da su.

Kara karanta wannan

Najeriya za ta yi nasara a yaki da rashin tsaro - Tinubu

Shi ma na ukunsu, Sanata mai wakiltar Kudancin Katsina, Bello Mandiya bai gabatar da wani korafi ko shawara a zaman fiye da shekaru biyu da rabi da ya yi ba.

Babba Kaita da Mandiyya sun zama Sanatoci ne a majalisa ta takwas. Babba-Kaita tsohon ‘dan majalisar wakilai ne, Mandiya ya yi aiki da gwamnan jihar Katsina.

Rahoton ya ce duk da haka, 1.4% da 0.2% na shawarwari da korafin da aka gabatar a majalisar dattawa daga 2019 zuwa 2021 suka fito daga Sanatocin jihar Arewar.

Osinbajo a Kano

An ji Farfesa Yemi Osinbajo ya yi magana a wajen wata lacca ta musamman da aka gabatar a jihar Kano inda ya yabi Marigayi Sardaunan Sokoto, Ahmadu Bello.

Mataimakin shugaban kasar ya kuma je gidan Alhaji Bashir Tofa ya yi masu ta'aziyya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng