Gwamnonin APC sun shiga ganawa yayin da rikicin kan taron gangamin jam'iyyar ya kazanta
- Gwamnonin jam'iyyar APC sun shiga ganawa kan rikicin jam'iyyar da ke sake rincabewa kafin gangamin zaben sabbin shugabannin jam'iyyar
- Gwamnonin da suka hallara sun hada da Zulum na jihar Borno, Matawalle na jihar Zamfara, Abdurrazaq na Kwara da sauransu
- Ana taron ne a masaukin gwamnan jihar Kebbi, Atiku Bagudu, da ke yankin Asokoro na babban birnin tarayya da ke Abuja
FCT, Abuja - Gwamnoni karkashin jam'iyya mai mulki ta All Progressives Congress (APC) sun shiga taro domin neman matsaya kan gangamin taron jam'iyyar da za a yi.
Ana taron ne a masaukin gwamnan jihar Kebbi da ke yankin Asokoro da ke Abuja, Daily Trust ta ruwaito.

Source: UGC
Rikici ya na cin jam'iyyar mai mulki tun bayan da kwamitin rikon kwarya na jam'iyyar karkashin jagorancin Gwamna Mai Mala Buni ya kasa shirya taron zaben sabbin shugabannin jam'iyyar.
A watan Nuwamban 2021, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gana da manyan shugabannin jam'iyyar a gidan gwamnati da ke Abuja, inda aka amince kan cewa za a yi zaben sabbin shugabannin jam'iyyar a watan Fabrairu, duk da ba a tsayar da rana ba.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Sakataren kwamitin rikon kwarya, Sanata John James Akpanudoedehe a wata takarda da ya fitar a makon da ya gabata, ya ce kwamitin ya na tuntubar masu ruwa da tsaki kafin taron, Daily Trust ta ruwaito.
Gwamnonin APC da suka halarci taron sun hada da; Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni; Babagana Zulum (Borno), Abubakar Badaru (Jigawa), Rotimi Akeredolu (Ondo), Abubakar Bello (Niger), Nasir El-Rufai (Kaduna), Kayode Fayemi (Ekiti), Yahaya Bello (Kogi), Ben Ayade (Cross River), Dapo Abiodun (Ogun).
Sauran sun hada da; Gwamnan jihar Zamfara , Bello Matawalle, David Umahi (Ebonyi), Gboyega Oyetola (Osun), Babajide Sanwolu (Lagos), Hope Uzodimma (Imo), Solomon Lalong (Plateau), Abdullahi Sule (Nasarawa), and Abdulraman Abdulrazaq (Kwara).
2023: Rikicin APC na cigaba da jagwalewa, ta kacame tsakanin Bagudu da Aliero
A wani labari na daban, rikici ya na ci gaba da kamari tsakanin gwamnan jihar Kebbi, Atiku Bagudu da Sanata Adamu Aliero wanda hakan zai janyo rabuwar kawuna a jam’iyyar APC a jihar, Daily Trust ta ruwaito a ranar Lahadi.
Shugabannin jam’iyyar na kasa da jihar sun bayyana wa manema labarai cewa, daga Bagudu har Aliero su na da wanda suke son a tsayar takarar gwamna a jam’iyyar APC.
Rahotanni sun nuna yadda Bagudu wanda shi ne shugaban kungiyar gwamnonin arewa ya ke so a daura antoni janar, Abubakar Malami a matsayin dan takara, yayin da Alieru wanda ya yi gwamna har sau biyu a jihar, yake son a tsayar da Yahaya Abdullahi, wanda shugaba ne na majalisar dattawa a dan takarar gwamnan jihar.
Asali: Legit.ng

