An gano dalilin kus-kus din Gwamnan APC da Tinubu sa'a 48 da ayyana niyyar takara

An gano dalilin kus-kus din Gwamnan APC da Tinubu sa'a 48 da ayyana niyyar takara

  • Gwamna Kayode Fayemi ya yi zama na musamman da Asiwaju Bola Tinubu a gidansa da ke Legas
  • Dr. Kayode Fayemi ya hadu da Bola Tinubu ne kwana biyu bayan ya bada sanarwar zai yi takara
  • ‘Yan siyasar sun tattauna a kan yadda za a samu tikitin APC da kuma takarar gwamnan jihar Ekiti

Lagos - A ranar Laraba, 12 ga watan Junairu, 2022, gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi ya zauna da jagoran APC na kudancin Najeriya, Asiwaju Bola Tinubu.

Jaridar Punch ta ce Dr. Kayode Fayemi ya sa labule da Asiwaju Bola Tinubu ne kan batun zaben fitar da gwani na jam’iyyar APC a zaben gwamnan jihar Ekiti.

Akwai zaben fitar da gwani a gaban APC a jihar Ekiti inda ake ganin Fayemi yana tare da Biodun Oyebanji, su Tinubu kuma suna goyon bayan Opeyemi Bamidele.

Kara karanta wannan

Shugaban kasa a 2023: Na shirya yin gaba da gaba da Tinubu a zaben fidda gwanin APC – Shahararren sanata

Haka zalika gwamnan da tsohon mai gidan na sa sun tattauna a game da batun takarar shugaban kasa na 2023, wanda Tinubu ya shaidawa Duniya zai yi takara.

Kudu maso yamma za su yi taron dangi

Majiya sun shaidawa jaridar cewa Fayemi ya yi magana da Bola Tinubu a kan batun burinsa na takara da tabbatar da cewa kasar Yarbawa aka kai tikitin APC.

Zaman shugaban kungiyar gwamnonin kasar da tsohon gwamnan na Legas ya sa an fara tunanin akwai yiwuwar ‘yan kudu maso yamma su hada-kansu.

Fayemi Tinubu
Gwamna Fayemi da Bola Tinubu
Asali: Facebook

‘Yan siyasar yankin za su iya fito da ‘dan takara daya domin ganin su aka tsaida takarar shugaban kasa.

Alakar Tinubu da Fayemi

Wani ‘dan siyasa da ya zanta da Punch bayan zaman, ya ce alakar Tinubu da gwamnan Ekiti ta tabarbare a lokacin Adams Oshiomhole yana rike da jam'iyyar APC.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Tsohon gwamna, kuma jigon jama'iyyar APC ya riga mu gidan gaskiya

Fayemi yana cikin wadanda suka dage sai da aka kori Oshiomhole, aka nada Mai Mala Buni.

Bayan haka, gwamnatin Fayemi tana gallazawa ‘yan kungiyar South West Agenda 2023 wanda suke yaki wajen ganin Bola Tinubu ya zama shugaban kasa a 2023.

Zan shiga takara - Tinubu

Ziyarar da Gwamnan ya kai wa Tinubu har gida ta zo ne jim kadan bayan ya je fadar shugaban kasa ya yi magana da Muhammadu Buhari kan batun tsayawa takara.

Ganin an shigo 2022, babban 'dan siyasar ya fito a mutum, ya bayyana shirinsa na harin tikitin neman kujerar shugabancin kasa a karkashin jam'iyyar APC mai mulki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng