Alao – Akala: Muhimman abubuwa 15 da ya dace a sani game da tsohon gwamnan Oyo

Alao – Akala: Muhimman abubuwa 15 da ya dace a sani game da tsohon gwamnan Oyo

Akala, tsohon gwamnan jihar Oyo ya rasu a ranar Laraba da safe. Mutuwarsa ta zo ne bayan wata daya da basaraken garin su ya rasu, Soun na Ogbomoso. Aloa-Akala yana daya daga cikin manyan ‘yan siyasar jihar Oyo.

Akwai abubuwa 15 muhimmai dangane da tsohon gwamnan da ya kamata a sani, Daily Trust ta ruwaito.

Otunba Adebayo Alao – Akala: Muhimman abubuwa 15 da ya dace a sani game da tsohon gwamnan Oyo
Otunba Adebayo Alao – Akala: Muhimman abubuwa 15 da ya dace a sani game da tsohon gwamnan Oyo. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC
  1. An haife shi a ranar 3 ga watan Yunin 1950 a Ogbomoso da ke karamar hukumar Ogbomoso da ke jihar Oyo.
  2. Aloa-Akala ya yi karatun firamaren shi a Makarantar Osuoa Baptist Day a Ogbomoso.
  3. Aloa-Akala ya ci gaba da karatu a makarantar barikin Kamina, Bataliya ta 5 a Infantry na Tamale, kasar Ghana.
  4. Ya zama Cadet Inspector na ‘yan sanda a watan Yunin 1974 a kwalejin ‘yan sandan Najeriya a Ikeja, Daily Trust ta ruwaito.
  5. Jami’in ‘yan sanda ne wanda ya yi ayyuka iri-iri a wurare daban-daban sannan ya yi murabus ya na mataimakin kwamishinan hukumar ‘yan sandan jihar Oyo, da ke Eleyele, Ibadan. Baya ga aikin gwamnati, ya yi kasuwanci.
  6. Shi ne mai TDB Global Ventures da kuma gidan rediyon Parrot FM da ke Ogbomoso a jihar Oyo.
  7. Ya fara siyasa a matsayin wata alkibla da ya dauka ta daban a rayuwarsa.
  8. Ya yi takara karkashin zero-party a zaben kananun hukumomi na 1996 sai kuma ya koma UNP daga bisani su ka yi majar jam’iyya da UNC inda ta dunkule zuwa UNCP. Ya shiga zaben fitar da gwani na mazabar Ogbomoso a karkashin UNCP a 1997.
  9. Ya tsaya takarar shugaban karamar hukumar Ogbomoso ta arewa inda ya ci, lokacin kansiloli 7 ne su ke karkashinsa a jam’iyyar APP a 1998. Daga nan ya zama mataimakin shugaban ALGON reshen jihar Oyo tsakanin 1999 da 2002.
  10. Alao-Akala ya samar da kungiyar hadin kan Ogbomoso, kungiyar da ta koma PDP daga baya. Ya kuma zama shugaban karamar hukumar Ogbomoso ta arewa a 1999 zuwa 2002.
  11. Ya yi mataimakin gwamnan jihar Oyo daga watan Mayun 2003 zuwa Janairun 2003. Bayan an cire gwamna Rashidi Ladoja, an rantsar da Alao-Akala a matsayin gwamna a watan Janairun 2006 inda ya yi watanni 11. A watan Disamban 2006 aka mayar da Rashidi Lakoja a matsayin gwamna bayan kotun koli ta kammala shari’arsu.
  12. Alao-Akala ya tsaya takarar gwamna a 2007 karkashin jam’iyyar PDP inda ya zama gwamna ya kammala mulki a watan Mayun 2011.
  13. A ranar 8 ga watan Disamban 2014, Alao-Akala ya koma jam’iyyar LP a jihar Oyo daga PDP.
  14. A ranar 10 ga watan Disamba 2014 ya bayyana burinsa na kara tsayawa takarar gwamnan jihar Oyo a watan Fabrairun 2015.
  15. A ranar 16 ga watan Disamban 2017 ya koma jam’iyyar APC inda aka yi shagali mai yawa a Ibadan, babban birnin jihar Oyo. Daya daga cikin yaransa, Olamiju Alao-Akala ya ci zaben shugaban karamar hukumar Ogbomoso.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Tsohon gwamna, kuma jigon jama'iyyar APC ya riga mu gidan gaskiya

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng