2023: Ubangiji ne yace in fito takara, bai bani tabbacin zan ci ba, Gov Dave Umahi
- Gwamnan jihar Ebonyi, Dave Umahi, a ranar Talata ya ce Ubangiji ne ya umarce shi da ya nemi takarar shugaban kasa a shekarar 2023
- Sai dai Gwamna Dave Umahi ya sanar da cewa, Ubangiji bai bashi tabbacin cewa zai lashe zaben ba idan ya fito takarar
- Bayan sa’o’i kadan da bayyana burinsa na fitowa takarar a karkashin jam’iyyar APC, ya bayyana a shirin inda ya yi wannan furucin
Ebonyi - Gwamnan jihar Ebonyi, Dave Umahi, a ranar Talata ya ce Ubangiji ne ya umarce shi da tsayawa takarar shugabancin kasa a 2023.
Umahi ya fadi hakan ne yayin da ya bayyana a wani shirin gidan talabijin din Channels na “Siyasar Mu a Yau”.
Ya bayyana a shirin ne bayan sa’o’i kadan da ya sanar da burinsa na tsayawa takara a karkashin jam’iyyar APC a gidan gwamnati da ke Abuja, bayan ganawarsa da shugaban kasa Muhammadu Buhari don ya sanar da burinsa na takarar.
Mr Umahi ya bayyana burinsa bayan sa’o’i 24 da jagoran jam’iyya APC, Bola Tinubu ya sanar da burinsa na tsayawa takarar.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Gwamnan Ebonyi ya ce Ubangiji ne ya ba shi umarni, amma bai sanar masa da ko zai ci ko ba zai ci nasara ba.
Kamar yadda yace:
“Ubangiji ne ya yi min magana- don haka akwai nasara. Na yi magana ne a lokacin da ya ba ni ikon yin maganar. Daga abinda Ubangiji ya ke yi a jihar mu, batun tattalin arziki, da taimakon Ubangiji mun samu nasarori wandanda mutane da dama su ke ganin kamar gwamnatin tarayya ce ta ba mu wata dama.
“Ka na magana da Ubangiji shi ma ya yi maka, addu’a kenan da kuma sauraron abinda Ubangiji ya ce a yi, kuma ina bin duk umarninsa. Ba Ubangiji ne ya ke fada maka za ka ci ko ba za ka ci nasara ba, a’a shirin duk nasa ne. Shirin Ubangiji zai nuna kan sa.”
Yayin da aka tambaye shi idan akwai yuwuwar ya kayar da sauran masu Jama’a a APC don tsayawa takara, Umahi cewa ya yi a shekarar 2020, ya bar PDP inda aka zabe shi har ya yi gwamna sau biyu, don haka mulki na Ubangiji ne. Kuma ya na ba wanda ya ga dama.
A cewarsa, ba abin mamaki bane yadda Ubangiji ya fito da mutum daga gidan yari ya zama shugaban kasa ba.
‘Yan siyasar Najeriya sun saba amfani da sunan Ubangiji musamman idan su na neman takara, kamar ta tsayawa shugaban kasa, Premium Times ta ruwaito.
A shekarar 2018, mai cocin Latter Rain Assembly wacce yanzu ake kira Citadel Community Church wacce ta ke a jihar Legas, ya ce Ubangiji ya ba shi umarnin tsayawa takarar shugaban kasa.
Bakare, wanda su ka tsaya takara tare da Buhari a takarar shugaban kasa da ya tsaya 2011 ya ce Ubangiji ya ce masa “Ba za ka iya kawo karshen siyasar ka ba.”
Ya kara da cewa:
“Joseph (na cikin Injila) bai tsaya takara ba; amma kuma ya zama firam ministan Egypt. Saboda me zan dami kai na a kan bin hanyoyi? Addu’o’i zan ta yi, a lokacin da Ubangiji ya so zai daura ni a matsayin da ya so.”
Bayan watanni 7 da Bakare ya yi wannan furucin, mai kula da cocin Household of God ya ce Ubangiji ya ba shi umarnin aika wa shugabannin jam’iyyun PDP da APC a kan su tsayar da shi takarar shugaban kasa a 2019.
Asali: Legit.ng