Karya ake yi mani na cewa ina shirin barin PDP, in sake komawa APC inji Rabiu Kwankwaso
- Tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso ya musanta raɗe-raɗin komawa jam’iyyar APC
- Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana haka ne a wata hira da ya yi da Channels TV a ranar Lahadi
- Kwankwaso ya tabo batun kiran da ake yi na cewa ya kama kujerar shugaban kasa ya bar Arewa a 2023
FCT, Abuja - An yi hira da tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso a game da batun da yake ta yawo na komawarsa jam’iyyar APC mai mulki.
A wata tattaunawa da ya yi da gidan talabijin na Channels TV, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso yace babu gaskiya a wannan jita-jita da yake ta yawo a yau.
A cewar Kwankwaso wanda ya yi gwamna a Kano, labarin karya ne kurum wasu suka kitsa. BBC ta fitar da wannan rahoto a ranar 9 ga watan Junairu, 2022.
Babban ‘dan siyasar yake cewa ya na murna da jin yadda wasu daga cikin mutanen da ya yi aiki da su a APC suke ta yada labarin dawowa jam’iyyar ta su.
“Ina farin cikin yadda mu ke ciki, mu na bakin kokarinmu a jam’iyyar PDP wajen ganin an samu nasara. Nan da karshen shekara, komai zai fito fili sosai”
“Siyasa na sauyawa, a da mu na APC, sai mu ka dawo PDP. Mu na cikin wadanda aka kafa jam’iyyar PDP da su a 1998, har na yi dacen zama gwamna.”
- Rabiu Kwankwaso
PDP tayi mani alheri
“A jam’iyyar PDP ne na zama gwamna a 1999, kuma na zama Ministan tsaro na kasa. Haka zalika a gwamnatinta ne nayi aiki a hukumar NDDC ta tarayya.”
Mulki ya koma kudu?
“Mutane su na cakuda abin da bai kamata a cakuda ba. Mu na da jam’iyyu dabam-dabam, inda kowace jam’iyya za ta kai takara, ya ragewa dabararta.”
"Idan aka duba zuwa 2023, jam’iyyar APC tayi mulkin shekara takwas, PDP kuma tayi 16. A cikin 16 da PDP tayi, Kudu tayi shekara 14, Arewa tayi biyu."
A dalilin haka, Kwankwaso yace ya ragewa kowace jam’iyya ta duba ta ga abin da za tayi domin ta kashe zabe, ba wai a tursasawa kowa inda zai kai takara ba.
Abiola, Obasanjo, Jonathan
A wannan hira da Seun Okinbaloye, Kwankwaso ya bayyana yadda ya rika marawa ‘yan takarar shugaban kasan da suka fito daga yankin kudancin Najeriya.
Asali: Legit.ng