2023: PDP ta yanke shawarar tsayar da dan takarar shugaban kasa daga arewa – Babangida Aliyu

2023: PDP ta yanke shawarar tsayar da dan takarar shugaban kasa daga arewa – Babangida Aliyu

  • Dr Babangida Aliyu, tsohon gwamnan jihar Neja, ya bayyana matsayin jam'iyyar PDP kan yankin da za ta mika tikitin takarar shugaban kasarta a zaben 2023
  • Aliyu ya ce babbar jam'iyyar adawar ta yanke shawarar sake mika tikitinta ga yankin arewacin kasar
  • Sai dai ya ce duk da hakan, sun yarda cewar dan takara daga kowani yankin kasar na iya neman kujerar

Niger - Tsohon gwamnan jihar Neja, Dr Babangida Aliyu, ya bayyana cewa jam'iyyar People’s Democratic Party (PDP) ta yanke shawarar sake mika tikitin shugaban kasa ga yankin arewa.

Hakan na zuwa ne duk da yarjejeniyar jam'iyyar adawar na cewa kowani dan takara zai iya tseren kujerar a zaben.

2023: PDP ta yanke shawarar tsayar da dan takarar shugaban kasa daga arewa – Babangida Aliyu
2023: PDP ta yanke shawarar tsayar da dan takarar shugaban kasa daga arewa – Babangida Aliyu Hoto: Premium Times
Asali: Facebook

Aliyu ya bayyana hakan ne a ranar Juma'a, 7 ga watan Janairu, lokacin da kungiyar goyon bayan Atiku suka ziyarce shi a garin Minna, Channels TV ta rahoto.

Kara karanta wannan

Kungiya ga Ortom: Ka mayar da hankali wurin biyan albashi a Benue, maimakon matsawa Buhari

Hakazalika tsohon gwamnan na Neja ya ce yana da yakinin nasarar kungiyar. Ya kuma basu tabbacin samun goyon bayansa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Aliyu ya ce:

"A yarjejeniyar ta shiyya-shiyya, mun yanke shawarar sake mika tikitin ga arewa kamar yadda saura suka bukata amma mun yarda a rubuta a bayyane sakamakon abun da ya faru cewa duk dan takara daga kowani yankin kasar na iya takarar wannan zabe."

Ya kara da cewa kungiyar tayi gagarumin kokari ta hanyar zuwa lungu da sakon kasar domin tabbatar da ganin cewa tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya zama dan takarar jam'iyyar kuma zababben shugaban Najeriya a 2023.

Jagoran kungiyar na kasa, Dr Victor Moses, ya yi godiya ga tsohon gwamnan kan goyon bayan da yake ci gaba da ba Atiku Abubakar har zuwa yanzu da 2023 ke gabatowa, rahoton The Nation.

Kara karanta wannan

Shugabancin APC: Ku hakura ku bar mun - Mustapha ya roki Almakura, Yari, Sheriff da sauransu

Yahaya Bello zai lallasa Atiku idan suka yi takarar zaben shugaban kasa tare a 2023 – Fani-Kayode

A gefe guda, tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode, ya bayyana cewa gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, zai kayar da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar idan suka yi takarar kujerar shugaban kasa tare a 2023.

Yayin da zaben 2023 ke kara gabatowa, ana ta rade-radi kan wadanda za su zamo yan takarar manyan jam'iyyun kasar guda biyu na All Progressives Congress (APC) da Peoples Democratic Party (PDP).

A wata da Channels TV a ranar Juma'a, Fani-Kayode ya ce ya yarda Bello zai zama 'nagartaccen shugaban kasa', inda ya kara da cewar gwamnan na Kogi zai tafi da matasan Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng