Sabon rikici ya kunno kai a APC yayin da fusatattun mambobin jam’iyyar suka maka Buni a Kotu

Sabon rikici ya kunno kai a APC yayin da fusatattun mambobin jam’iyyar suka maka Buni a Kotu

  • Rikicin cikin gida na kara kamari a APC kan babban taron jam'iyyar mai zuwa a watan Fabrairu
  • A yanzu haka, wasu fusatattun mambobin jam'iyyar mai mulki sun maka kwamitin riko na jam'iyyar karkashin jagorancin Mai Mala Buni a kotu
  • Sun nemi kotu da dakatar da duk wani abu da ya danganci gudanar da babban taron har sai bayan an kammala taurukan jihohi

Abuja - Rikicin da ya dabaibaye jam'iyyar All Progressives Congress (APC) kan babban taron watan Fabrairu ya kara kamari.

Jaridar Punch ta rahoto cewa wasu mambobin jam'iyyar sun maka kwamitin riko wanda Mai Mala Buni ke jagoranta a gaban wata babbar kotun tarayya da ke Abuja.

Masu karar sun nemi umurnin kotu don dakatar da kwamitin da Buni ke jagoranta daga gudanar da babban taron.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari ya rantsar da sabbin mambobin kwamitin jagorancin NNPC

Sabon rikici ya kunno kai a APC yayin da fusatattun mambobin jam’iyyar suka maka Buni a Kotu
Sabon rikici ya kunno kai a APC yayin da fusatattun mambobin jam’iyyar suka maka Buni a Kotu Hoto: APC
Asali: UGC

Dama dai kungiyar gwamnonin APC sun shirya wani taro a karshen makon nan a Abuja, wanda za a yi a masaukin gwamnan jihar Kebbi da ke Asokoro.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shugaban kungiyar gwamnonin na APC kuma gwamnan jihar Kebbi, Atiku Bagudu, ya ce babban manufar taron shine taron jam'iyyar da aka shirya a watan Fabrairun 2022.

An yi ta yamutsa gashin baki kan sauya ranar babban taron jam'iyyar na kasa da ake shirin yi.

Amma wadanda suka shigar da karar a ranar 4 ga Janairu, 2022, su ne Suleiman Dimas Usman, Muhammed Shehu, Samaila Isahaka, Idris Isah, da Audu Emmanuel.

An lissafo APC, shugaban kwamitin riko na APC da hukumar zabe mai zaman kanta, cikin mutane 1-3 a takardar shari’ar wanda ‘yan jarida suka samu a Abuja ranar Juma’a.

Masu kara a shari'ar mai lamba FHC/ABJ/CS/3/2022, ta hannun lauyansu Olusola Ojo, sun nemi umurnin kotu na dakatar da taron bisa hujjar cewa ba a riga an kammala taruka a dukka jihohi 36 na tarayya ba.

Kara karanta wannan

Shugabancin APC: Ku hakura ku bar mun - Mustapha ya roki Almakura, Yari, Sheriff da sauransu

Masu karar sun gabatar da tambayoyi biyar da kotun za ta tantance sannan kuma sun nemi sassaucin furuci guda takwas, rahoton Sahara Reporters.

Wasu daga cikin sassaucin sun hada da umarnin wannan kotu na hana wadanda ake kara na 1 da na 2 shiryawa da gudanar da babban taron kasa na wanda ake kara na daya har sai dai idan an fara kammala taron jihohi a fadin jihohi 36 na tarayya da kuma babban birnin tarayya Abuja.

Sun kuma nemi umurnin kotu da ke umartan wadanda ake kara na 1 da na 2 da su fara gudanar da taron jiha na wanda ake kara na 1 a jihar Anambra da jihar Zamfara kafin a shirya da gudanar da babban taron kasa.

Shugabancin APC: Ku hakura ku bar mun - Mustapha ya roki Almakura, Yari, Sheriff da sauransu

A wani labarin, tsohon mataimakin Shugaban rusasshiyar jam’iyyar Congress for Progressive Change (CPC) na kasa kuma babban dan takarar kujerar shugaban APC na kasa, Saliu Mustapha, ya nemi sauran yan takara da su janye masa.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Wasu jiga-jigan PDP a jihohi 24 sun zabi Atiku ya gaji Buhari, inji Dokpesi

Mustapha ya bukaci da su lamunce masa a matsayin dan takara na bai daya, jaridar Daily Trust ta rahoto.

Ya yi rokon ne a ranar Alhamis, 6 ga watan Janairu, a Abuja lokacin da manyan Jami’an gwamnati daga jihar Nasarawa suka kai masa ziyara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng