2023: Najeriya na bukatar wanda zai kawo hadin kai kamar Atiku, Dokpesi
- Raymond Dokpesi, tsohon shugaban kafar sadarwa ta Daar, ya ce ya kamata shugaban kasar Najeriya na gaba ya hada kan kasar
- A cewar Dokpesi, Najeriya ba ta taba rabewa ba, don haka Najeriya ta na bukatar mutum kamar Atiku Abubakar ne, tsohon mataimakin shugaban kasa, ya mulke ta
- Dama a watan Oktoban da ya gabata, Dokpesi ya ce babu wani dan takara daga kudancin Najeriya da zai iya lashe zaben shugaban kasa na 2023
Raymond Dokpesi, tsohon shugaban kafar sadarwa ta Daar ya ce ya kamata shugaban kasan da zai gaji mulki a 2023 ya kasance wanda zai hade kan kasar, TheCable ta ruwaito.
Dokpesi ya ce Najeriya ba ta taba rabuwa ba, inda ya kara da cewa kasar nan ta na bukatar mutum kamar Atiku Abubakar ne, tsohon mataimakin shugaban kasa, ya mulki kasar yadda ya dace.
“Yanzu da 2023 ta ke karatowa, tattalin arzikin kasar ya tabarbare gaba daya kuma yaranmu sun rasa ayyukan yi,” a cewarsa.
“Gaskiya mu na bukatar wanda zai hade kan kasa, tsayayyen mutum, wanda ya san kan dukiya don samun damar rike kasar nan da kyau kamar Atiku.”
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Kamar yadda TheCable ta ruwaito, ya kara da cewa:
“Kan kasar nan bai taba rabuwa ba kamar yanzu, a bangaren addini da al’adu. Yanzu haka tattalin arziki ya kara lalacewa. Ba a taba cin bashi daga waje da cikin kasa ba kamar yadda aka yi a cikin shekaru 6 zuwa 7 da APC ta ke shugabancin kasa ba.
“Abinda mu ke ta fuskanta karkashin mulkin Buhari shi ne yadda ake ta halaka yaranmu. Rashin tsaro da ta’addanci duk ya dabaibaye ko ina.”
A watan Oktoban da ya gabata, Dokpesi ya ce babu wani dan takara daga kudu da zai iya cin zaben shugaban kasa a 2023. Duk da gwamnonin kudu sun bijiro da bukatar ko wacce jam’iyya ta tsayar da dan takararta daga kudu.
Ba zan saki Nnamdi Kanu ba, ya kare kan shi a gaban kotu, Buhari
A wani labari na daban, Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya ce shugaban 'yan awaren IPOB, Nnamdi Kanu, ya gurfana a gaban kotu tare da kare kansa a kan labaran karya da ya dinga yadawa a kasashen ketare kan mulkinsa.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce shugaban dan a waren IPOB, Nnamdi Kanu, ya kare kansa gaban kotu akan yada karairayi dangane da mulkinsa lokacin ya na kasashen ketare.
Buhari ya furta hakan ne yayin wata tattaunawa wacce gidan talabijin din Channels ta nuna a ranar Laraba kuma Legit.ng ta kula da shi.
Asali: Legit.ng