Gwamna ya yi watsi da Tinubu Atiku da Saraki, ya faɗi wanda yan Najeriya za su zaba a 2023

Gwamna ya yi watsi da Tinubu Atiku da Saraki, ya faɗi wanda yan Najeriya za su zaba a 2023

  • Gwamnan jihar Abia ya bayyana cewa lokaci ya yi da ɗan ƙabilar Igbo zai jagoranci Najeriya matukar adalci za'a yi
  • Gwamna Okezie Ikpeazu, yace yana goyon bayan takarar tsohon shugaban majalisar dattawa, Sanata Anyim, a zaben 2023
  • Anyim yace ya kai ziyara jihar Abia ne domin sanar da gwamna da shugabannin PDP na jiha kudirinsa

Abia - Gwamna Okezie Ikpeazu na jihar Abia ya nuna goyon baya ga tsohon shugaban majalisar dattawa kuma tsohon SGF, Anyim Pius Anyim, ya zama shugaban ƙasa na gaba daga yankin Igbo.

Punch tace gwamnan ya yi wannan furucin ne a gidansa dake Umuobiakwa, karamar hukumar Obingwa, yayin da ya karbi bakuncin Anyim ranar Lahadi.

Ya bayyana shi da, "Mutum wanda kwarewarsa da gogewarsa ta dace da kujerar shugaban ƙasa a Najeriya."

Kara karanta wannan

Akwai abubuwa masu kyau dake jiran yan Najeriya a sabuwar shekara, Gwamna Masari

Gwamna jihar Abia, Okezie Ikpeazu
Gwamna ya yi watsi da Tinubu Atiku da Saraki, ya faɗi wanda yan Najeriya za su zaba a 2023 Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

Lokaci ya yi da Igbo zai jagoranci Najeriya

Ikpeazu ya tabbatar wa Anyim cewa yana goyon bayansa 100% ya zama shugaban ƙasa na gaba daga yankin kudu maso gabashin Najeriya.

Ya kuma kara da cewa abin da ya dace a yi a wannan lokacin shi ne, "A baiwa Igbo dama su fitar da shugaban ƙasa na gaba."

Gwamnan yace:

"Ba bu wata kabila da ta nuna kaunar dunƙulewar Najeriya ƙasa ɗaya a aikace kamar Igbo, kamar yadda kowa ke gani mutanen mu na rayuwa kuma su zuba dukiyarsu a kowane sashi na ƙasar nan."

Meya kai Anyim jihar Abia?

Tun da farko, Sanata Anyim ya bayyana cewa ya zo da kansa ne domin ya sanar da gwamna Ikpeazu da kuma shugabancin PDP na jihar kudirinsa na tsayawa takarar shugaban ƙasa a 2023.

Kara karanta wannan

Ko ta wane hali sai jam'iyyar PDP ta samu nasara a babban zaben 2023, Gwamna

A cewarsa, kudu maso gabas ne ya fi dacewa ya fitar da shugaban ƙasa na gaba, matukar aka duba dai-daito da kuma adalci, kamar yadda Ripples Nigeria ta ruwaito.

Tsohon sanatan ya kara da cewa ya yanke shawaran neman takara ne bayan dogon nazari a kan kwarewarsa da kuma shawarin masu ruwa da tsaki a kowane bangaren kasar nan.

Daga nan kuma ya bukaci goyon bayan gwamna da PDP reshen jihar, tare da tabbatar musu da cewa ba zai ba su kunya ba idan ya zama shugaban ƙasa.

A wani labarin na daban kuma Gwamna Wike na jam'iyyar PDP ya tsallake Atiku, ya bayyana wanda yake ganin PDP zata baiwa takara daga Arewa a 2023

Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, yace jam'iyyar PDP na da damar lashe zaɓen shugaban ƙasa a 2023, matukar takwaransa na jihar Bauchi, Bala Muhammed, ta tsayar takara.

Wike yace yan Najeriya daga kowane sashi, lunu da sako na ƙasar nan na kira ga PDP ta tsayar da gwamna Bala Muhammed na Bauchi a 2023.

Kara karanta wannan

Ministan Buhari ya fara shirye-shiryen tsayawa takarar shugaban ƙasa a 2023

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262