Gwamnan PDP ya tsallake Atiku, ya bayyana wanda PDP zata baiwa takara daga Arewa a 2023

Gwamnan PDP ya tsallake Atiku, ya bayyana wanda PDP zata baiwa takara daga Arewa a 2023

  • Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas yace Allah ba zai gafarta wa PDP ba matukar jam'iyyar ta sake watsi da kiran yan Najeriya
  • Wike yace yan Najeriya daga kowane sashi na kira ga PDP ta tsayar da gwamna Bala Muhammed na Bauchi a 2023
  • Yace wannan shine lokacin da ya dace PDP ta sake ɗarewa kan mulkin Najeriya domin ceto kasar daga halin da ta faɗa

Bauchi - Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, yace jam'iyyar PDP na da damar lashe zaɓen shugaban ƙasa a 2023, matukar takwaransa na jihar Bauchi, Bala Muhammed, ta tsayar takara.

Gwamnan ya yi wannan furucin ne yayin da yake amsa tambayoyin yan jarida lokacin da ya kai ziyara jihar Bauchi ranar Asabar.

Punch ta rahoto Wike na cewa Allah ba zai gafarta wa jam'iyyar PDP ba matukar ta gaza cika burin yan Najeriya na komawa kan mulkin kasa.

Kara karanta wannan

Daga karshe: Shehu Sani ya bayyana aniyar tsayawa takarar gwamna, ya fadi manufarsa

Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike
Gwamnan PDP ya tsallake Atiku, ya bayyana wanda PDP zata baiwa takara daga Arewa a 2023 Hoto: gazettengr.com
Asali: UGC

Daily Nigerian ta rahoto Wike yace:

"Ɗan uwana, Bala, na da kwarewa sosai. Ya rike darakta a ma'aikata kacokan, ya zauna kujerar sanata, sannan ya tafi minista kuma yanzun ga shi a matsayin gwamna. Wannan kaɗai ya isa ya zama shugaban ƙasa."
"Sannan idan ka duba abin da yake yi a Bauchi a zangon mulkinsa na farko, ni ƙaina na zo nan ne na kaddamar da aikinsa, ga takwarorina sun zo yin haka, gwamnoni nawa suka yi haka a zangon farko?"
"Bala ya cancanta ya nemi kujerar shugaban ƙasa, ya zarce duk yadda ake tunani. A hange na idan ka duba alaƙarsa da sauran mutane babu kamarsa. Dan haka mutane na bukatar ya zama shugaban ƙasa ne dan ya cancanta."

Lokaci ya yi da PDP zata ceto Najeriya

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Yan bindiga sun yi awon gaba da tsohon dan takarar gwamna a jihar Arewa

Wike ya koka cewa Najeriya ta tsinci kanta cikin gagarumin rikici saboda rashin tsaro, inda ya kara da cewa lokaci ya yi da PDP zata koma kan madafun iko ta ceto ƙasar nan.

"Daya daga cikin abin da na ƙudurta a shekarar 2022 shi ne Najeriya ta samu cigaba fiye da shekarar da ta gabata, kuma mu tabbatar PDP ta haɗa kanta."
"Saboda idan muka sake kuskuren watsi da bukatar yan Najeriya, zai yi wahala Allah ya gafarta mana."

A wani labarin na daban kuma Wike ya bayyana yadda aka cafke shi da mahifinsa da sauran iyalan gidansu bisa zargin kisa

A wurin taron karin shekara na babban lauya, Emmanuel C. Ukala, (SAN), gwamna Wike ya bada labarin yadda iyalan gidansu baki ɗaya suka sgiga hannun hukuma kan zargin kisa.

Haka nan kuma gwmanan ya bayyana yadda aka sake kam shi a karo na biyo da zargin yana da hannu. a aika fashi da makami.

Kara karanta wannan

Kukah: Lokacin zaɓe ne kaɗai ƴan Najeriya suke tuna addini banda lokacin sata

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262