Clark ga Lai Mohammed: Jonathan ne ya kori Boko Haram daga LGAs 14 a Borno ba Buhari ba

Clark ga Lai Mohammed: Jonathan ne ya kori Boko Haram daga LGAs 14 a Borno ba Buhari ba

  • Edwin Clark, fitaccen dan siyasa, ya karyata Lai Mohammed, ministan yada labarai da al'adu na kasar nan kan cewa da yayi Buhari ya kora Boko Haram
  • Clark ya kafa hujja da littafin Jonathan inda ya bayyana cewa, gwamnatinsa ce ta kori Boko Haram daga kananan hukumomi 14 na Borno
  • Clark ya ce abun kunya ne yadda Mohammed ke zabga karya duk da kokarin gwamnatin baya, wanda ba don haka ba ko zabe ba za a iya yi ba

Delta - Mulkin tsohon shugaban kasa Goodluck Joonathan ne ya kori 'yan ta'addan Boko Haram daga kananan hukumomi goma sha hudu kafin zaben 2015 daga inda suke rike da su a jihar Borno, ba kamar yadda ministan yada labarai, Lai Mohammed, ya fadi ba.

Kara karanta wannan

Buhari ga hafsoshin tsaro: Ku murkushe Boko Haram kafin 2023

Dattijon dan siyasa, Chief Edwin Clark, ya bayyana hakan a wata takarda da ya fitar a ranar Talata inda yace kokarin mulkin da ya gabata ne ya bayar da damar yin zabe a yankunan, Tribune Online ta ruwaito.

Clark ga Lai Mohammed: Jonathan ne ya kori Boko Haram daga LGAs 14 a Borno ba Buhari ba
Clark ga Lai Mohammed: Jonathan ne ya kori Boko Haram daga LGAs 14 a Borno ba Buhari ba. Hoto daga tribuneonlineng.com
Asali: UGC
Clark ya ce, takardar da ministan ya fitar tsabar karya ce da ya zuga inda yace "Da yanzu Najeriya ta zama kasar daular Boko Haram idan da ba don shugaban kasa Muhammadu Buhari ba."
Kamar yadda tsohoon kwamishinan yada labaran ya ce "'Yan Najeriya ba su karba wannan tsabar karyar ba na cewa gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ce ta kora Boko Haram daga kananan hukumomi goma sha hudu na jihar Borno."

Tribune Online ta ruwaito cewa, ya debo daga cikin littafin Jonathan inda yace tsohon shugaban kasan ya bayar da labarin yadda suka kori Boko Haram:

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Ganduje ya ziyarci fadar Buhari, ya ce gwamnoni suna bukatar taimako

"Duk da haka, makonni shidan sun yi mana amfani, mun karba kayan aikin sojoji da muke jira kuma a cikin wannan lokacin, sojojin mu sun yi abun jinjina inda suka ragargaji 'yan ta'adda tare da kwato yankunan Najeriya da suke hannunsu a baya. An durkusar da Boko Haram har zuwa lokacin da na mika mulki ga magaji na a 2015.
"Mun kammala zabe hankali kwance, ko da kuwa akwai wasu al'amura, a kalla hankalin 'yan kasa ya kwanta kan cewa an yi zabe cikin kwanciyar hankali kuma babu rikicin bayan zabe."

Kamar yadda Clark yace, babu dan kasa nagari da zai yarda da maganganun Mohammed kan cewa karbar mulkin Buhari ne ya hana Boko Haram kafa gwamnatinsu a Najeriya.

"'Yan Najeriya masu tarin yawa sun yarda cewa gwamnatinsa ce ta bayar da damar da muguwar kungiyar ta dawo da kuma zafin ta," yace.

Obasanjo ga Clark: Niger Delta ba ta isa ta nuna iko kan man fetur din Najeriya ba

Kara karanta wannan

Ziyarar Maiduguri: Abubuwa 3 da na ke so magajina ya yi idan ya karbi mulki - Buhari

A wani labari na daban, tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, ya ce dukkan man fetur da ke yankin Niger Delta na Najeriya ne kuma yankin bai isa ya nuna iko kan fetur ba matukar suna cikin Najeriya.

Daily Trust ta ruwaito cewa, Obasanjo ya ce kowanne ma'adanai da ke kowanne bangare na kasar nan mallakin kasar ne ba na yankin ba.

Ya sanar da hakan ne yayin martani ga fitaccen shugaban kabilar Ijaw, Edwin Clark, wanda ya zargi cewa Obasanjo ya tsani yankin Niger Delta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng