Shahararren Malamin addinin musulunci a jihar Kano ya fice daga jam'iyyar APC
- Fitaccen malamin addinin Islama a Kano, Sheikh Ibrahim Khaleel, ya rubuta takardan murabus daga mamban APC
- Shehin Malamin yace ya jima yana son fita daga jam'iyyar amma majalisar malamai na shiga tsakani ta sasanta
- A baya dai malamin ya yi fatali da mukamin SA wanda gwamnatin jihar Kano ta ba shi
Kano - Shahararren malamin addinin musulunci a jihar Kano, Malam Ibrahim Khaleel, ya bayyana ficewarsa daga jam'iyyar APC mai mulki.
Shehin Malamin ya shaida wa jaridar Dailytrust cewa ya rubuta takardar murabus daga APC duk da har yanzun bai miƙa ta ga shugabannin jam'iyya ba.
Ya ƙara da cewa dalilin da yasa bai miƙa takardar murabus ɗin ba shi ne saboda rikicin dake faruwa a APC reshen Kano, wanda a yanzu yake gaban kotu, ana buga shari'a.
Malamin yace:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Na rubuta takardan murabus ɗina daga jam'iyyar APC kuma ina jiran hukuncin da kotu zata yanke kan rikicin shugabanci dake faruwa tsakanin ɓangarori biyu."
"A wannan lokacin zan mika takardar murabus ɗina ga shugabannin da aka tabbatar."
Malamin ya ƙara da cewa ya so ficewa daga jam'iyyar tun a watan Nuwamba, amma da majalisar malamai ta jihar Kano ta saka baki ne ya ja hankalinsa ya fasa.
Meyasa ya fita daga APC kuma wace jam'iyya zai koma?
Sheikh Khaleel ya bayyana cewa ba zai faɗi ainihin abin da yasa ya ɗauki matakin fita daga jam'iyyar ba ko kuma jam'iyyar da zai koma.
Legit.ng Hausa ta tattaro muku cewa a baya malamin ya yi fatali da mukamin bai bayar da shawari na musamman (SA) da gwamnatin APC ta jihar Kano ta ba shi.
Haka nan kuma Malamin na da hannun a a rikicin dake faruwa tsakanin majalisar malamai da kuma gwamnatin jihar Kano.
A wani labarin na daban kuma Shugaba Buhari ya rantsar da sabon karamin minista a fadarsa Aso Rock
Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari , ya rantsar da sabon karamin ministan ayyuka da gidaje, Muazu Sambo, a fadarsa dake birnin tarayya Abuja.
A farkon wannan makon, majalisar tarayya ta amince da naɗin Mua'zu Sambo a matsayin sabon minista, bayan shugaba Buhari ya aike musu da sunan shi.
Asali: Legit.ng