Tsohon gwamnan Kaduna, Ramalan Yero, Ya bayyana shirinsa na tsayawa takara a zaben 2023

Tsohon gwamnan Kaduna, Ramalan Yero, Ya bayyana shirinsa na tsayawa takara a zaben 2023

  • Tsohon gwamnan Kaduna, Ramalan Yero, yace a halin yanzun wuƙa da nama na hannun mutane su tantance tsakanin PDP da APC
  • Yero, wanda ya sha kaye a hannun El-Rufai a 2015, yace mutane sun gwada PDP na shekara 16, sun kuma gwada APC na shekara 8
  • Tsohon gwamnan yace zai dawo ya sake neman takarar gwamnan jihar Kaduna a babban zaɓen 2023 dake tafe

Kaduna - Gabanin zaɓen gwamnan jihar Kaduna dake tafe a 2023, tsohon gwamna, Mukhtar Ramalan Yero, yace zai sake neman ɗarewa kujerar gwamna.

Vanguard ta ruwaito Yero na cewa a halin yanzun al'ummar Kaduna sun gane banbancin dake tsakanin jam'iyyar PDP da kuma APC.

Yero yace:

"Ya rage ga mutane su yanke hukunci tsakanin mulkin PDP tsawon shekara 16 da kuma mulkin jam'iyyar APC na shekara 8, wanne ya fi a gare su."

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Gwamnonin Arewa ta Gabas sun shiga ganawar sirri a Yobe

Ramalan Yero
Tsohon gwamnan Kaduna, Ramalan Yero, Ya bayyana shirinsa na tsayawa takara a zaben 2023 Hoto: bbc.com
Asali: UGC

Yero wanda shi ne a kujerar gwamnan Kaduna a 2015 lokacin da ya sha ƙasa a hannun Malam Nasir El-Rufai, yace zai sake neman komawa gwamna a 2023.

Meyasa zai sake tsayawa takara?

A wata hira, tsohon gwamnan yace:

"Mutanen jihar Kaduna sun jaraba jam'iyyar PDP na tsawon shekara 16, yanzun sun ɗanɗana jam'iyyar APC na shekara 8. Ko tantama babu yanzun sun gane banbancin."
"PDP ta kwashe shekara 16, amma APC a shekara 8 kun ga irin halin da kuke ciki. Dan haka ku auna ku gani, lokacin PDP ne ya fi, ko kuma na APC.
"Idan mulkin jam'iyyar PDP ya fi, to ya kamata ku koma mata ku tabbata kun sake kaɗa wa PDP kuri'unku."

Wane halin mutanen Kaduna suke ciki yanzu?

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: An tsinci gawar wani matashi da mace a cikin mota tsirara

Tsohon gwamnan ya kara da cewa mutane sun rasa ayyukansu, dukiyoyinsu, kasuwancinsu, gidajensu kuma suna rayuwa cikin tsoro.

"Ina shawartan mutane su koma su zaɓi PDP. Zan tsaya takarar gwamnan a zaɓen 2023, a baya da na rike gwamna, ina ɗaya daga cikin waɗanda suƙa sauke nauyin mutane fiye da wannan gwamnatin."

A wani labarin na daban kuma kuma Jami'an DSS da Yan Sanda sun garkame Press Center a Kano

Hukumomin tsaro da suka haɗa da yan sanda, DSS da sauransu, sun rufe sakateriyar NUJ (Press Centre) a jihar Kano

Jami'an sun ɗauki wannan matakin bayan gano ana shirin amfani da wurin domin gudanar da zanga-zangan lumana kan tabarbarewar tsaro a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262