Ba dalilin da zai sa APC ta sha ƙasa a zaben 2023 domin yan Najeriya na jin dadin mulkin Buhari, Gwamna
- Gwamna Hope Uzodimma na jihar Imo ya bayyana cewa ba dalilin da zai hana APC samun nasara a babban zaɓen 2023 dake tafe
- Gwamnan yace duba da namijin kokarin da gwamnatin Buhari ke yi duk da kalubalen da take fuskanta ya isa yaba APC nasara
- Yace har yanzun mutane turuwar shiga APC suke, kuma jihohi 22 na ƙasar nan na karkashin jam'iyya mai mulki
Imo - Gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma, yace babu dalilin da zai sa APC ta gaza kai banten ta a zaɓen 2023 kasancewar gwamnatin Buhari na aikin da ya dace.
Gwamnan ya yi wannan magana yayin hira da manema labarai na gidan gwamnati ranar Talata jim kaɗan bayan ganawa da shugaba Buhari a Aso Rock.
A cewarsa, a baya-bayan nan jam'iyyar APC ta samu karuwa a mambobinta, kamar yadda The Cable ta ruwaito.
Gwamnan yace:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Wane yanayi aka shiga da zai hana jam'iyyar APC samun nasara? Ko kuna son nuna mun baku san jihohi 22 na hannun APC ba? Ko bakusan mafi yawan kananan hukumomin kasar nan na karkashin APC ba? Shin baku ga yadda ake dandazon shigowa APC ba?"
"Yanayin da ake ciki a kasar nan ya nuna shugaban ƙasa na yin abinda ya dace duba da matsalar tsaron da ta addabi duniya, ga annobar korona ta mamaye ko ina, daga wannan nau'in zuwa wannan."
"Ina da tabbaci kuma ina alfahari da kasancewana mamban APC. Ina tunanin zamuyi duk me yuwuwa wajen tabbatar da bamu baiwa yan Najeriya kunya ba saboda yaƙinin su a kan mu."
Shin APC zata kalubalanci zaɓen Anambra a Kotu?
Ya kara da cewa shugabancin APC na kasa ne zai ɗauki matakin kan kalubalantar zaɓen Farfesa Soludo a zaɓen jihar Anambra.
Uzodimma, wanda shine shugaban yakin neman zaɓe a Anambar, yace sakon murnan da shugaba Buhari ya aike wa Soludo ba shi ke tabbatar da APC da ɗan takararta ba zasu ɗauki matakin shari'a ba.
"Andy Uba ya garzaya kotu ko bai kai kara kotu ba, wannan ba shi da alaƙa da shugaban ƙasa. Dokar da ta baiwa INEC damar sanar da sakamako, ita ta baiwa yan takara kalubalantarsa a kotu."
A wani labarin kuma Mataimakin shugaban masu rinjaye na majalisar dokokin jihar Filato ya yi murabus daga mukaminsa
Honorabus Dasun, yana daga cikin makusantan tsohon kakakin majalisa da aka tsige kwanakin baya, Abuk Nuhu Ayuba, kuma ya sanar da murabus ɗinsa ne ranar Talata.
Majalisar dokokin jihar Filato ta tsinci kanta cikin rikicin siyasa tun bayan tsige tsohon kakakinta, Honorabul Abok.
Asali: Legit.ng