2023: Ta kacame tsakanin gwamnonin APC kan batun fitowa takarar Tinubu

2023: Ta kacame tsakanin gwamnonin APC kan batun fitowa takarar Tinubu

  • Sanata Rufai Hanga, tsohon jigon jam'iyyar APC ya fallasa rikicin da ke faruwa tsakanin gwamnonin jam'iyya mai mulki kan hangen kujerar shugaban kasa
  • A cewar Hanga, akwai wurin tsagi uku zuwa hudu na gwamnonin wadanda kowanne tsagi ya na da burin da ya ke hange a 2023 kuma ba za su sassauta ba
  • Ya ce daya daga cikin tsagin ya nada wani gwamna da ministan Buhari domin takara, yayin da wani tsagin ke bayan Tinubu kuma sun ce ba za su zama 'ya'yan kaji ba

Kafin zuwan zaben shugabancin kasa na 2023, sabon rikci ya barke tsakanin gwamnonin jam'iyyar All Progressives Congress (APC) kan burin tsohon gwamnan jihar Legas, Asiwaju Bola Tinubu, kan maye gurbin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar APC ta bayyana matakin da zata ɗauka kan Ganduje da Shekarau bayan hukuncin Kotu

Duk da har yanzu Tinubu bai bayyana bukatarsa na fitowa takarar shugabancin kasa ba, yana ta tuntubar fitattun 'yan Najeriya tare da ziyartarsu domin neman goyon baya, Independent.ng ta ruwaito.

2023: Kawunan gwamnonin APC sun rabu kan batun fitowa takarar Tinubu
2023: Kawunan gwamnonin APC sun rabu kan batun fitowa takarar Tinubu. Hoto daga independent.ng
Asali: UGC

Fitaccen dattijon kasa, a cikin kwanakin nan Tinubu ya ziyarci Alhaji Tanko Yakasai a Abuja, ya bayyana masa burinsa na maye gurbin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

A yayin zantawa da Daily Independent a Abuja, Sanata Rufai Hanga, asalin wadanda suka kafa tsohuwar jam'iyyar Congress for Progressive Change (CPC) kuma jigon APC, wanda ya bar jam'iyyar cikin kwanakin nan, ya ce an samu rabuwar kai tsakanin gwamnonin jam'iyyar mai mulki kan batun shugabancin kasan.

Kamar yadda yace, yayin da wasu gwamnonin jam'iyyar suke hararo daya daga cikinsu matsayin dan takara, tare da wani ministan Buhari a matsayin mataimaki, wasu na ganin cewa Tinubu ya cancanci halacci kan abinda yayi wa jam'iyyar.

Kara karanta wannan

Matasan Najeriya ba su shirya karbar shugabanci ba, Mamban APC

Ya ce, "Muna da tsagi uku zuwa hudu kuma babu yuwuwar hade kansu. Gwamnonin jam'iyyar ne wadanda suke wani hange kuma ba su da niyyar sassautawa.
"A takaice, a kwanaki uku da suka gabata, na ji daga majiya mai karfi cewa wasu gwamnoni sun zabi daya daga cikinsu kan ya fito takarar shugabancin kasa. Sun zabi abokin takararsa daga cikin ministoci kuma ba su da burin hakuri.
"Akwai gwamnonin da ba su son jin wannan. Wadannan su ne gwamnonin da ke son Tinubu. Wadannan suna cewa abun takaici ne yadda za a saka wa Tinubu duk da tikin da yayi wa jam'iyyar. Suna kiran takwarorinsu da kada su zama dan kaza ci ka goge baki."

Matasan Najeriya ba su shirya karbar shugabanci ba, Mamban APC

A wani labari na daban, mamba a jam'iyyar All Progressives Congress (APC) reshen jihar Ribas, Karibi Bob Manuel, ya ce matasan Najeriya ba su da ra'ayin bibiyar shugabanninsu domin karbar shugabanci.

Kara karanta wannan

Majalisa ta gayyaci shugaban INEC kan batun kudade N500bn na zaben fidda gwani

Bob Manuel ya sanar da kamfanin daillancin labaran Najeriya a Fatakwal jihar Ribas a ranar Juma'a cewa, yanayin yadda matasa ke martani kan manyan abubuwan da ke faruwa a kasar nan ne ya nuna hakan, Daily Trust ta ruwaito.

"Muna cikin wani hali wanda matasa suke nuna kamar komai daidai tare da sakarcin bibiyar shugabannin siyasa ba tare da wani tunani ba.
"Matasa suna yi kamar wasu wadanda aka siya ko kuma marasa alkibla wadanda a koyaushe ake juya mu son rai tamkar sakako kuma ake nuna mana abinda ya dace mu yi," ya jajanta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng