2023: Kotu zata yanke hukunci kan ko Atiku ya cancanci tsayawa takarar shugaban kasa
- Kotu ta sa ranar 21 ga watan Fabrairu na shekara mai kamawa 2022 a matsayin ranar yanke hukunci kan ƙarar da aka shigar da Atiku
- Wata kungiya a nahiyar Afirka (EMA) ta shigar da karar dake kalubalantar Atiku ya nemi kujerar shugaban kasa a Najeriya
- Sai dai gwamnatin Adamawa ta shiga cikin shari'ar kuma ta fede biri har wutsiya kan ainihin inda Atiku ya fito
Abuja - Babbar kotun tarayya dake Abuja, ta sa ranar 21 ga watan Fabrairu, 2022 domin yanke hukunci kan ko Atiku Abubakar, na da damar neman kujera lamba ɗaya a Najeriya.
Tribune Online ta rahoto cewa alkalin kotun, mai sharia Inyang Ekwo, shine ya sanar da ranar bayan gama sauraron kowane bangare.
A kara mai lamba FHC/ABJ/CS/177/2019, wata kungiya ta Nahiyar Afirka, (EMA) ta gurfanar da Atiku, jam'iyyar PDP, hukumar zaɓe INEC, da Antoni Janar na kasa.
EMA ta kalubalanci cewa Atiku ba shi da damar neman kujerar shugaban ƙasar Najeriya kasancewar ba'a Najeriya aka haife shi ba.
Kungiyar ta nemi kotu ta dakatar da waɗan nan mutanen da sauran su, duba da sashi na 25(1) & (2) da kuma sashi na 131(a) na kundin tsarin mulkin Najeriya.
Hakanan kuma kungiyar tace bisa abinda kundin ya ƙunsa da kuma yanayin rashin tabbas na ainihin inda aka haifi Atiku, bai cancanci neman kujera lamba ɗaya ba.
Gwamnatin Adamawa ta shiga shari'an
A ranar 27 ga watan Yuli, gwamnatin jihar Adamawa ta Ofishin Antoni Janar, ta nemi kotu ta saka ta cikin waɗan da ake ƙara.
Kotun ta baiwa Antoni Janar na jihar Adamawa damar shiga cikin shari'ar a matsayin wanda ake ƙara na biyar.
Gwamnatin Adamawa ta shaida wa kotun cewa Atiku Abubakar ya cancanci ya tsaya takarar shugaban ƙasa a Najeriya, kamar yadda Premium Times ta rahoto.
Bugu da ƙari ta faɗa wa kotun cewa Atiku ɗan asalin jihar Adamawa ne, wanda aka zaɓe shi gwamnan jihar a 1999, daga bisani ya rike mukamin mataimakin shugaban ƙasa daga 1999-2007.
"Wannan karar da aka shigar tauye haƙƙi ne ba wai ga Atiku kaɗai kada ya taka takarar shugaban ƙasa ba, ga baki ɗaya al'ummar jihar Adamawa."
A wani labarin na daban kuma Jam'iyyar APC ta lashe zaben kananan hukumomi 16 da kansiloli a jihar Ekiti
Jam'iyyar APC ta samu nasara a baki ɗaya kujerun da aka fafata a zaben kananan hukumomin jihar Ekiti.
Shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta, Jide Aladejana, yace APC ta lashe kujerun ciyamomi 35 da kansiloli 176 cikin 177.
Asali: Legit.ng