Da addu'a zamu karbi mulkin Najeriya, matar Atiku ta magantu kan shirinsu a zaben 2023
- Da alamu dai tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar yana samun goyon bayan iyalansa domin tsayawa takara a 2023
- Daya daga cikin matan Atiku, Misis Titi Abubakar ta ce babu laifi ya ci gaba da yunkurinsa na zama shugaban kasa
- ‘Ya’yan Atiku ma, a lokuta daban-daban, sun nuna cewa mahaifinsu zai tsaya takarar shugaban kasa a 2023
Yola, Adamawa - Misis Titi Abubakar, uwargidan tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, ta bayyana cewa za ta kara masa kwarin gwiwar sake tsayawa takarar shugaban kasa a karo na biyu a zaben 2023.
Atiku haifaffen jihar Adamawa yana yunkurin zama shugaban Najeriya tun a shekarun 1990.
Akwai jita-jita cewa shahararren dan siyasan zai sake lalubar damar tsayawa takara a zaben 2023.
Uwargidansa Titi, ‘yar asalin jihar Osun, ta ce da ikon Allah, mijinta zai zama shugaban kasa a Najeriya.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ta shaida wa jaridar The Punch cewa:
“Lokacin da mijina yake makaranta, ya shiga siyasa. Kuma da zarar ka zama dan siyasa, za ka ci gaba da zama dan siyasa. Eh, yana siyasa tun zamanin MKO Abiola, amma kaddara ce. Idan Allah ya ce lokaci bai yi ba, babu abin da mutum zai iya yi. Ka ci gaba da gwadawa.
“Allah ya ce mu yi addu’a ba kakkautawa, kuma za mu ci gaba da addu’a. Idan zuciyarka na son abu, ka ci gaba da addu'a ga Allah da nacewa akai, har sai ya ba ka abin da kake so. Don haka, ba zan iya gaya wa mijina kada ya yi siyasa ba. Watakila, Allah ya ce wannan shi ne lokacin da ya dace da shi.”
Dalilin da yasa Atiku ya yi aure daga kabilu daban-daban
A kwanakin baya ne Atiku ya bayyana dalilansa na yin aure daga sassa daban-daban na kasar nan.
Ya dora alhakin matsalolin da kasar nan ke fama da su a kan yadda shugabannin siyasa na kabilanci da addini suke amfani da su wajen darewa kan karagar mulki, yana mai nuni da cewa salon aurensa alama ce ta imaninsa ga daukacin ‘yan Najeriya ba tare da la’akari da kabila ko addini ba.
Ya kara da cewa dan Najeriya mara kabilanci ne kadai zai iya kawo hadin kai a kasar.
A wani labarin, daya tsagin kwamitin tsare-tsare na taron gangami na musamman (CEPC) a jam’iyyar APC mai mulki a ranar Litinin da ta gabata, ya yi zargin cewa wasu jiga-jigan jam’iyyar ‘yan jam’iyyar adawa ta PDP ne.
Kwamitin ya kuma ce suna sanya rigar jam’iyyar APC mai mulki ne kawai don su lalata kudurin jam'iyyar.
Daily Trust ta ruwaito cewa kungiyar Progressive Youth Movement (PYM) ta kaddamar da sabon kwamitin CEPC a Abuja, a ranar Litinin.
Asali: Legit.ng