Dalilin da yasa muka nemi yan sanda sun cafke hadimin Danjuma Goje, Jam'iyyar APC ta magantu
- Jam'iyyar APC mai mulki ta bayyana dalilin da yasa ta nemi yan sanda su cafke hadimin Sanata Danjuma Goje
- Kakakin APC reshen jihar Gombe, Moses Kyari, yace jam'iyya ta ɗauki mataki kan Yayari ne saboda yaɗa ƙanzon kurege a soshiyal midiya
- Haka nan yace babu hannun gwamna Inuwa Yahaya na jihar Gombe a zancen kama hadimin tsohon gwamnan
Gombe - Jam'iyyar APC reshen jihar Gombe, a ranar Alhamis, ta bayyana dalilin da yasa ta nemi jami'an yan sanda su cafke Mohammed Adamu Yayari, hadimin Sanata Ɗanjuma Goje.
Dailytrust ta rahoto APC na cewa ta ɗauki wannan matakin ne saboda Yayari ya zuzuta da ƙara yawan shugabannin APC da suka yi murabus a makon da ya gabata.
Sakataren watsa labarai da hulɗa da jama'a na APC a jihar Gombe, Mista Moses Kyari, shine ya bayyana haka a wurin taron manema labarai ranar Alhamis.
Ya kuma yi zargin cewa rubutun da Yayari ya yi game da murabus ɗin shugabannin APC na Gombe Goje ne ya saka shi.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Kazalika Mista Kyari ya bayyana cewa an kirkiri rubutun ne a gidan ɗaya daga cikin manyan hadiman Goje, Danjuma Babayo.
Kyari yace:
"Sun kira taron shugabannin APC a gidan Babayo, inda suka nemi haɗin kan su, domin su koma bayan Goje, amma babu wata maganar Murabus."
"Amma abun takaici da ban haushi, nan da nan Mohammed Yayari ya garzaya kafar sada zumunta ya rubuta karerayinsa."
APC ta ɗauki mataki kan Yayari
Kyari ya bayyana cewa daga nan APC ta kai karar su ga yan sanda, bayan zababbun shugabannin APC na ƙaramar hukumar Yamaltu/Deba sun rubuto takardar korafi a kan mutanen biyu.
A cikin takardan sun zargi Babayo da Yayari da ruruta abu bisa cewa kaso 80 cikin 100 na shugabannin APC a karamar hukumar sun yi murabus.
Bugu da ƙari, Mista Kyari yace babu hannun gwamnan jihar Gombe, Muhammad Inuwa Yahaya, a kame hadimin Goje.
A wani labarin kuma Jigon PDP ya bayyana sunayen gwamnan APC da tsohon gwamna dake shirin sauya sheka zuwa PDP
Jigon jam'iyyar hamayya PDP a jihar Abia, Dakta Nkole, ya gargaɗi PDP kada ta karbi Sanata Kalu da gwamnan Ebonyi.
A cewarsa waɗan nan mutanen sun gano cewa sun yi kuskuren sauya sheka zuwa APC shiyasa suke son dawo wa PDP.
Asali: Legit.ng