Anambra: Jam'iyyun siyasa 11 ne suka maka Soludo a kotun karar zabe

Anambra: Jam'iyyun siyasa 11 ne suka maka Soludo a kotun karar zabe

  • Jam'iyyun siyasa tare da 'yan takara 11 ne suka maka Farfesa Charles Soludo da jam'iyyar APGA a gaban kotun sauraron kararrakin zabe
  • Akwai jam'iyyyun siyasan da ke bukatar kotun da ta soke zaben baki daya sakamakon matsalar da aka samu da na'urar BVAS
  • Sai dai kamar yadda mai bai wa Gwamna Obiano shawara ya sanar, jam'iyyar APGA baccin ta ta ke har da munshari duk da karar ta da aka kai

Anambra - Jam'iyyun siyasa tare da 'yan takara sun mika korafi inda suke kalubalantar nasarar dan takarar jam'iyyar All Progressives Grand Alliance, APGA, Farfesa Charles Soludo a zaben gwamna da aka yi a jihar Anambra.

Masu korafin sun yi gaggawar mika korafin kafin cika kwana 21 bayan zaben kamar yadda sakataren kotun sauraron kararrakin zabe, Surajo Gusau ya sanar.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Kotu ta kori karar da ke neman soke takarar gwamna na Soludo a Anambra

Vanguard ta ruwaito cewa, ya ce jam'iyyun sun mika korafe-korafensu ne tsakanin Litinin zuwa Talata, a lokacin da ba a yi tsammanin cewa akwai 'yan takarar da aka lallasa ba da zasu kalubalanci nasarar Soludo.

Anambra: Jam'iyyun siyasa 11 ne suka maka Soludo a kotun karar zabe
Anambra: Jam'iyyun siyasa 11 ne suka maka Soludo a kotun karar zabe. Hoto daga Vanguardngr.com
Asali: UGC

Wadanda suka mika kokensu gaban kotun sun hada da Sanata Andy Uba na jam'iyyar APC wanda ke bayyana cewa shi ke da kuri'u mafi rinjaye da aka kada a zaben.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Akwai jam'iyyar Action Democratic Party (ADP) da dan takarar ta, Prince Adam Ume-Ezeoke wanda ke bukatar kotun da ta soke zaben sakamakon matsalar da aka samu da na'urar BVAS.

Hakazalika, dan takarar jam'iyyar Accord, Dr Godwin Maduka da jam'iyyarsa suna bukatar a soke zaben saboda matsalolin da aka samu, yayin da dan takarar jam'iyyar United Patriots, UP, ya yi korafi saboda an cire sunansa daga cikin 'yan takara.

Kara karanta wannan

An dakatad da Shugaban APC a Anambra kan laifi 'ya yiwa Buhari rashin kunya

Sauran jam'iyyun da suka mika korafi a gaban kotun sun hada da Green Party da Action People’s Party APP.

Alkalai uku da za su yi shari'ar za su hallara ne a jihar Anambra a mako mai zuwa domin su fara zama, Vanguard ta ruwaito.

A yayin jawabi kan wannan cigaban a Awka, mai bada shawara na musamman ga Gwamna Willie Obiano kan lamurran siyasa, Chief Ifeatu Obiokoye, ya ce jam'iyyarsu ta APGA bacci ta ke har da munshari kan wannan korafe-korafen.

Kotu ta kori karar da ke neman soke takarar gwamna na Soludo a Anambra

A wani labari na daban, The Nation ta ruwaito cewa, wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yi watsi da karar da ta nemi a soke takarar gwamna da mataimakan gwamna na jam’iyyar APGA a zaben gwamnan da ya gabata a jihar Anambra.

Legit.ng Hausa ta tattaro cewa, karar an shigar da ita kan dan takarar APGA da ya lashe zabe, Charles Soldu da mataimakinsa Onyeka Ibezim.

Kara karanta wannan

An hana yaron Marigayi Muammar Gaddafi neman kujerar Shugaban kasa a zaben Libya

Masu shigar da kara – Adindu Valentine da Egwudike Chukwuebuka – suna zargin Soludo da Ibezim sun bayar da bayanan karya a cikin takardar da suka mika wa hukumar INEC don haka a bayyana cewa ba su cancanci tsayawa takara ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng