Thebo Mbeki: Yadda na yi kutun-kutun na hana Obasanjo zarcewa karo na 3
- Bincike ya kara bayyana yadda aka shiga aka fita don ganin an dakatar da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo yin mulkin Najeriya a karo na uku
- Tsohon shugaban Afirka ta kudu, Thabo Mbeki, ya bayyana yadda shi da tsohon shugaban kasa Abdulsalami Abubakar su ka jajirce wurin hana shi
- Obasanjo ya dade ya na musanta cewa ya na cikin wadanda suka bukaci a gyara kundin tsarin mulkin kasa wanda zai ba shi damar mulkin Najeriya a karo na uku
Bincike ya ci gaba da bayyana yadda burin tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo na mulkar Najeriya a karo na uku ya ki tabbata, Daily Trust ta ruwaito hakan.
Tsohon shugaban kasan Afirka ta kudu, Thabo Mbeki ya bayyana yadda shi da tsohon shugaban kasan Najeriya, Abdulsalami Abubakar suka hada kai wurin hana Obasanjo zarcewa karo na 3.
Obasanjo ya dade ya na musanta zama cikin wadanda suka bukaci gyara a kundin tsarin mulkin Najeriya wanda zai amince ya mulki Najeriya a karo na uku.
Daily Trust ta ruwaito cewa, yayin hira da Abdulsalami ta yanar gizo a ranar Alhamis a taron Festschrift da aka yi a Abuja, Mbeki ya ce ya kira tsohon shugaban kasan don tattaunawa da shi.
A cewarsa:
“Dama ce kafa jaddada jajircewar janar Abubakar a dimokradiyyar Najeriya a 2006, fiye da shekaru 5 bayan na mika karagar mulki ga Olusegun Obasanjo, kundin tsarin mulkin Najeriya ne ya bayar da damar Obasanjo ya yi mulki sau biyu kuma an zabe shi don ci gaba da mulki zuwa 2007.
“Amma akwai wani lokaci a 2005 da ya fara kamfen a Najeriya don kundin tsarin mulkin Najeriya ya ba shi damar shugabanci a karo na uku. Bisa wannan bukatar ne ya gabatar da bukatar gyaran gaban majalisar tarayya.
“Bayan na ji wannan labarin ne na bukaci tattaunawa da Obasanjo don kwaba masa akan wannan bukatar tasa. Daga baya na tattauna da jam'ar Abubakar kuma mun tsaya akan hana wannan bukatar ta shi. Saboda bama so a bata tsarin Najeriya da sauran nahiyoyi.
“Mun yarda da hade bakunanmu wurin hana yin wannan gyara a kundin. Mun yarje akan Abdulsalami zai jajirce tare da ni wurin hana gyaran. Na kuma ji dadin yadda ya yi kira ga majalisar tarayya akan kin amincewa da bukatar tasa.”
Tsohon Shugaban Majalisa ya rubuta littafi, ya tona asirin Obasanjo na neman zarcewa a mulki
A wani labari na daban, Punch tace tsohon Ministan tsaro kuma babban sojan Najeriya, Janar Theophilus Y. Danjuma ya yabi litaffin ‘Standing Strong’ da Ken Nnamani ya rubuta.
Sanata Ken Nnamani ya rubuta wannnan litaffi na ‘Standing Strong’ domin ya yi bayanin irin yunkurin da Olusegun Obasanjo ya yi na tsawaita wa’adinsa a kan mulki.
Janar Theophilus Danjuma wanda ya yi aiki da Obasanjo a lokacin da ya yi mulki a 1999 da zamanin soja tsakanin 1976 da 1979, shi ne wanda ya kaddamar da littafin.
Asali: Legit.ng