2023: Abin da zai hana mu lashe zaben Shugaban kasa da Gwamnonin jihohi inji Jigon PDP
- Babbar Jam’iyyar hamayya a Najeriya watau PDP ta na iya cigaba da zaman adawa bayan 2023
- Umar Sani yace idan PDP ba ta canza halinta ba, to babu mamaki APC ta sake yin galaba a kanta
- Hadimin tsohon mataimakin shugaban kasar ya bayyana matsalolin da suke damun jam’iyyar PDP
Abuja - Jam’iyyar hamayya ta PDP ba ta da tabbacin karbe mulki a jihohi da gwamnatin tarayya a zabe mai zuwa na 2023, a cewar Alhaji Umar Sani.
Daily Trust ta rahoto Umar Sani yana wannan bayani a wajen wani taron manema labarai da aka shirya a Abuja, a ranar 24 ga watan Nuwamba, 2021.
Sani wanda shi ne mai ba tsohon mataimakin shugaban kasa, Namadi Sambo shawara a kan harkokin yada labarai yace PDP na fuskantar kalubale.
A cewar ‘dan siyasar, jam’iyyar PDP mai hamayya ta gamu da sabani a kusan kowane mataki, wanda hakan ya jawo mata rabuwar kai a jihar Kaduna.
Yadda PDP ta barke a Kaduna
A halin yanzu akwai bangarenAhmad Makarfi, da bangaren mai gidan Umar Sani watau Namadi Sambo da kuma wasu ‘yan tafiyar Restoration movement.
Jaridar ta rahoto Sani yana cewa a sama, gwamnonin jihohi sun yi kabe-kabe, har sun yi sanadiyyar korar shugaban jam’iyya, Prince Uche Secondus.
“Idan Uche Secondus ya yi nasara a kotu, hakan ya na nufin shugabannin jam’iyyar da aka zaba sun tashi aiki, kuma hakan matsala ne ga shirin 2023.”
“Muddin jam’iyyar PDP ba ta daina kama-karyarta ba, ta sasanta cikin gidanta, hakan zai yi tasiri wajen gaza komawanta kan mulki.” - Umar Sani.
Rashin tsaro a Najeriya
A zantawar da ya yi da ‘yan jarida a birnin tarayya Abuja, Sani wanda da su aka kafa jam’iyyar ta PDP a 1998 ya koka a kan matsalar tsaro da ake fama da ita.
Alhaji Sani ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta kawo karshen matsalar rashin tsaro a kasar nan.
Abba gida gida v Ganduje
Kwanan nan wani Jagoran APC a Kano, Nura Hussaini Ungogo ya fallasa yadda aka murde zaben 2019 domin gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya zarce a 2019.
Nura Hussaini Ungogo ya fito ya shaidawa Duniya yadda APC ta koma mulki, inda yace da zaben gaskiya aka ayi, da tuni Abba Kabiru Yusuf ne gwamnan jihar.
Asali: Legit.ng