Kafa Ƙasar Biafra Da Oduduwa: Tsohon Mai Neman Takarar Shugaban Ƙasa Daga Arewa Ya Goyi Bayan Kanu da Igboho

Kafa Ƙasar Biafra Da Oduduwa: Tsohon Mai Neman Takarar Shugaban Ƙasa Daga Arewa Ya Goyi Bayan Kanu da Igboho

  • Adamu Garba, tsohon mai neman tikitin takarar shugabancin kasa ya ce ba laifi bane Nnamdi Kanu da Sunday Igboho su nemi ballewa daga Nigeria
  • Garba ya bada misalin kasashe kamar Rasha inda ta bawa wasu jihohinta dama suka kafa kasashensu kuma a halin yanzu suna zama lafiya
  • Tsohon mai neman takarar shugaban kasar ya ce ba kuma laifi bane masu son kafa jam'iyyar musulunci su kafa idan har za su mutunta kundin tsarin mulkin kasa

Tsohon mai neman tikitin takarar shugabancin kasa, Adamu Garba, ya ce wadanda ke neman balllewa daga Nigeria su kafa kasashen Biafra da Oduduwa suna da ikon yin hakan, Daily Trust ta ruwaito.

Kafa Ƙasar Biafra Da Oduduwa: Tsohon Mai Neman Takarar Shugabancin Ƙasa Ya Goyi Bayan Nnamdi Kanu da Igboho
Tsohon Mai Neman Takarar Shugabancin Ƙasa Ya Goyi Bayan Nnamdi Kanu da Igboho. Sodiq Adelakun
Asali: Original

Da ake hira da shi a daren ranar Laraba a shirin Daily Politics na Trust TV, ya ce ba laifi bane a kirkiri wata kasar daga Nigeria, amma akwai bukatar dogaro da kundin tsarin mulki.

Kara karanta wannan

An tafi har gida an bindige Shugaban kamfanin Three Brothers Mill da matarsa a Jigawa

Ya ce:

"Rasha ta fuskanci irin wannan lamarin kamar Indonesia. Yanzu idan ka tafi Rasha. Akwai jihohi guda 82 a Rasha; 22 daga cikinsu tamkar wasu kananan kasashe ne. Mazabar ke zaben shugaban kasarsu sannan Moscow ta tabbatar da shi a matsayin shugaba.
"Me zai hana mu yi amfani da irin tsarin? Idan 'yan Biafra sun ce suna son Biafra, menene matsala idan an samu Jamhuriyar Biafra cikin Tarayyar Nigeria? menene matsala idan an samu Jamhuriyar Oduduwa cikin Tarayyar Nigeria? Menene matsala idan an samu jam'iyyar musulunci a Borno? Babu wani matsala idan an yi hakan. Akwai jam'iyyun musulunci daban-daban a kasashen musulunci."

Garba ya cigaba da cewa:

"Idan ka ce kana son ka kafa jam'iyyar musulunci kuma ka kafa gwamnati, ka yi hakan kuma ka zabi gwamna amma dole ka girmama kundin tsarin mulkin tarayyar Nigeria."

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Sojoji sun fatattaki 'yan bindiga daga wani gari a Kaduna

"Idan ka yi hakan, za ka gano cewa kana magance matsalar sannan zaka samar da zaman lafiya mai dorewa."

Dan takarar gwamna ya sharɓi kuka a bainar jama'a yayin yaƙin neman zaɓe a Anambra

A wani rahoton, dan takarar gwamna na jam'iyyar Zenith Labour Party (ZLP) da za a yi a ranar 6 ga watan Nuwamba, Dr Obiora Okonkwo, ya zubar da hawaye a yayin da ya ziyarci garin Okpoko don kaddamar da aikin titi na miliyoyin naira a ranar Laraba.

Aikin titin zai fara ne daga Ede Road, School Road/Awalite da Ojo street ya tsaya a Owerri road a garin Okpoko a karamar hukumar Ogbaru a jihar ta Anambra, Daily Trust ta ruwaito.

Okonkwo ya zubar da hawaye ne a lokacin da ya ga wata mata mai shayarwa mai shekaru 30 wadda ta fada cikin kwata bayan ta kasa bin titin saboda rashin kyawunsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164