Shekarau, Barau, Sha’aban da sauran ‘Yan taware sun bada sharudan yin sulhu da Ganduje

Shekarau, Barau, Sha’aban da sauran ‘Yan taware sun bada sharudan yin sulhu da Ganduje

  • Kwamitin sulhun da jam’iyyar APC ta kafa a karkashin Sanata Abdullahi Adamu ya fara aiki a Najeriya
  • Wasu daga cikin fusatattun ‘yan jam’iyyar APC sun gabatar da takardar korafi gaban kwamitin NRC
  • A jihohin Kwara da Imo, ‘yan tawaren APC sun ki bada damar ayi masu sulhu da gwamnoninsu

Abuja - Wasu daga cikin kusoshin jam’iyyar APC da suke rikici da gwamnoninsu, sun gabatar da takardunsu gaban kwamitin sulhu na kasa da aka kafa.

Jaridar Daily Trust tace ‘yan tawaren sun gabatar da takardunsu ne a gaban shugaban kwamitin NRC, tsohon gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Adamu.

A makon da ya gabata ne Sanata Abdullahi Adamu ya yi kira ga fusatattun ‘ya ‘yan jam’iyyar APC su kawo korafinsu domin uwar jam’iyya ta dauki mataki.

Fusatattun ‘yan jam’iyyar APC a jihar Kano a karkashin jagorancin tsohon gwamna, Sanata Ibrahim Shekarau sun gabatarwa NRC da koke-koken na su.

Kara karanta wannan

Babban darasin da APC ta koya a zaben Gwamnan Anambra inji Tsohon Hadimin Buhari

Ibrahim Shekarau yana tare da takwaransa Sanatan Kano ta Arewa da wasu mutane biyar wajen fada da bangaren jam’iyyar APC da ke tare da gwamnatin Kano.

Da Daily Trust ta tuntubi mai magana da yawun bakin Sanatan na Kano ta tsakiya, Dr. Sule Ya’u Sule, yace korafinsu ya kai gaban kwamitin tun a ranar Talata.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

APC a Kano
Buhari yana kamfe a Kano Hoto: www.pulse.ng
Asali: UGC

Babu sulhu a Kwara da Imo

A jihar Kwara, mutanen Ministan labarai da al’adu, Lai Mohammed sun ce ba za su kai kuka gaban NRC ba, duk da rigimarsu da gwamna Abdulrahman Abdulrazaq.

Daya daga kusoshin bangaren Lai, kuma babban ‘yan adawan gwamna a yankin jihar Kwara ta kudu, Alhaji Abdulraheem Akorede, yace ba za su amsa gayyata ba.

“Da farko dai Sanata Adamu bai gayyace mu ba, kuma ko ya yi, ba za mu je ba, ko mu aika masa takarda. Ba mu yarda kwamitinsa zai yi abin kirki ba.” – Akorede.

Kara karanta wannan

Gumi ya caccaki 'yan aware: Igboho da Kanu ne suka kunna wutar rikicin Fulani a kudu

Akasin wannan ya faru a Legas, inda ‘yan tafiyar Lagos4Lagos movement suka ce sun yarda kwamitin na Abdullahi Adamu zai yi masu adalci a jam’iyya.

A jihar Imo, shugaban tsagin Rochas Okorocha watau Daniel Nwafor ya tuburewa kwamitin sulhun.

Ana so uwar jam'iyya ta dauki mataki

Kwanakin baya aka ji cewa Gwamnonin APC suna so ai Mala Buni ya hukunta wadanda suka bangare, suka ja daga a zaben shugabannin jihohi da aka gudanar.

Akwai jihohin da aka samu shugabanni fiye da daya a zaben shugabanni na APC. Irinsu Ibrahim Shekarau, Amosun, Rochas Okorocha ba su tare da gwammnoninsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng