Yanzu-Yanzu: Daga ƙarshe, INEC ta ayyana wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar Anambra
- Hukumar zabe mai zaman kanta INEC ta ayyana Farfesa Charles Soludu na jam'iyyarAPGA a matsayin zakaran zaben gwamnan Anambra na 2021
- Soludo, tsohon gwamnan babban bankin Nigeria CBN ya samu jimillar kuri'u 112,229 inda ya doke masu biye masa na PDP da APC
- Dan takarar na jam'iyyar APGA ya doke masu faffatawa da shi a kananan hukumomi 19 cikin 21 da ke jihar ta kudu maso gabas
Anambra - Hukumar Zabe mai zaman kanta INEC ta ayyana dan takarar jam'iyyar All Progressives Grand Alliance (APGA) Prof Charles Soludo a matsayin wanda ya yi nasara a zaben gwamnan jihar Anambra.
Shugaban Jami'ar Calabar, (UNICAL), kuma baturen zaben na Anambra, ya sanar da cewa Soludo ne zabeben gwamna misalin karfe 1.51 kamar yadda Daily Trust ta rahoto.
Tsohon gwamnan babban bankin na Nigeria ya zamu jimillar kuri'u 112,229 hakan ya bashi damar zama zakara.
Valentine Ozigbo na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ne ya zo na biyu da kuri'u 53,807.
An tabbatar wa Soludo na nasararsa ne bayan an kidaya kuri'un da aka kada a karamar hukumar Ihiala.
Soludo ya lallasa Ozigbo da ƙuri'u fiye da 5,000 a ƙaramar hukumar Ihiala
Chukwuma Soludo, ɗan takarar gwamna ka jam'iyyar All Progressive Grand Alliance (APGA) a zaben Anambra ya lashe zaɓen ƙarashe da aka yi ƙaramar hukumar Ihiala.
Jaridar The Cable ta ruwaito cewa an sanar da sakamakon zaɓen ne a ranar Laraba.
Hukumar zabe mai zaman kanta, INEC, ta dakatar da tattara ƙuri'un zaben gwamnan da aka yi a ranar 6 ga watan Nuwamba ne bayan gabatar da sakamakon ƙananan hukumomi 20 cikin 21.
Florence Obi, baturen zaɓen, ya sanar da cewa za a ƙarasa zabe a ƙaramar hukumar Ihiala tunda ba a samu ikon yi ba a ranar 6 ga watan Nuwamba.
Da ya ke gabatar da sakamakon zaben a ranar Laraba, baturen zaɓen ya ce an samu ƙallubale a rumfunan zaɓe biyu inda jami'an zabe suka gaza shiga garin saboda 'tirjiyya'.
Soludo ya samu ƙuri'u 8,283, sai kai biye masa Valentine Ozigbo na jam'iyyar People's Democratic Party PDP da ya samu ƙuri'u 2,485.
Jam'iyyar Young Progressive Party, YPP, ta samu ƙuri'u 344 sai All Progressive Congress, APC, ta samu 343.
Ga dai cikakken bayanin yadda sakamakon zaɓen ya ke.
Wadanda suka yi rajistan zabe - 148,361
Wadanda aka tsabtace su - 12,298
A- 261
AA- 07
AAC- 08
ADC- 11
ADP- 30
APC -343
APGA - 8,283
APM- 13
APP - 06
BP - 13
LP - 105
NNPP - 06
NRM - 06
PDP - 2,485
PRP- 09
SDP- 60
YPP- 344
ZLP- 12
Ƙuri'u masu kyau da aka kaɗa - 12,002
Ƙuri'u marasa kyau - 267
Jimillar ƙuri'u da aka kaɗa - 12,269
Asali: Legit.ng