Da duminsa: Soludo ne a sahun gaba, APGA ta lashe kananan hukumomi 16 a Anambra
- Alamu na nuna cewa jam'iyyar APGA ba ta shirya tattara komatsan ta ba da barin gidan gwamnatin jihar Anambra ba
- Farfesa Chukwuma Soludo ne a halin yanzu ya ke gaba bayan an bayyana sakamakon zabe a kananan hukumomi 16 na jihar
- Kamar yadda INEC ta sanar, Soludo ya na da kuri'u 99,765, Ozigbo ya na da kuri'u 44,543 sai Uba da ya ke kuri'u 48,305.
Anambra - Akwai manyan alamun da ke nuna cewa jam'iyyar All Progressives Grand Alliance ba ta da niyyar tattara komatsanta ta bar gidan gwamnatin jihar da ke Awka a jihar Anambra.
Farfesa Chukwuma Soludo, dan takarar jam'iyyar a zaben gwamnan shi ke gaba inda ya lashe zabe a kananan hukumomi sama da biyu bisa uku na jihar, Daily Trust ta wallafa.
Sanata Ifeanyi Uba na jam'iyyar Young Progressives Party (YPP) da Valentine Ozigbo na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) sun yi nasarar lashe kananan hukumomi daddaya.
A bangaren Sanata Andy Uba na jam'iyyar All Progressives Congress (APC), har yanzu bai lashe zaben ko karamar hukuma daya ba, Daily Trust ta wallafa.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ana jiran sakamakon kananan hukumomi biyu kafin a kammala tare da sanar da sakamakon karshe.
Duk da akwai kananan hukumomi 21 a jihar Anambra, hukumar zabe mai zaman kanta ta INEC ta bayyana cewa ba a yi zabe ba a karamar hukumar Ihiala ta jihar.
A dukkan sakamakon, Soludo ya na da kuri'u 99,765 a kananan hukumomi 16 na jihar, Ozigbo ya na da kuri'u 44,543 sai Uba da ya ke kuri'u 48,305.
Asali: Legit.ng