Yanzu Yanzu: An fara zabe a Awka da kewaye bayan an tsaurara matakan tsaro

Yanzu Yanzu: An fara zabe a Awka da kewaye bayan an tsaurara matakan tsaro

  • Masu zabe sun fara kada kuri'arsu a yawancin yankunan Awka, babbar birnin jihar Anambra bayan an girke matakan tsaro a yankin
  • Kafin jami'an tsaron su ba mutum damar wucewa, sai sun bincike shi tare da nuna masu katin zabensa
  • Sai dai kuma duk da haka, akwai karancin masu kada kuri'a a rumfunar zabe kamar yadda wakilin Legit.ng ya gano a birnin

Jihar Anambra - An fara gudanar da zabe a yawancin yankunan Awka, babbar birnin jihar Anambra inda aka girke jami'an tsaro da yawa a yankin.

Jami'an tsaro sun kuma fara binciken mutane da ababen hawan da ke ketarawa a yawancin yankunan babbar birnin jihar, inda suka bukaci su nuna katin zabensu kafin su basu damar wucewa.

Yanzu Yanzu: An fara zabe a Awka da kewaye bayan an tsaurara matakan tsaro
Yanzu Yanzu: An fara zabe a Awka da kewaye bayan an tsaurara matakan tsaro
Asali: UGC

Wakilin Legit.ng wanda ke yawon karade birnin ya lura cewa har yanzu mutane basu fito ba sosai domin yin zaben.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Masu zaben gwamnan Anambra sun yi biris, sun ki fitowa daga gidajensu don yin zabe

A wata rumfar zabe a Okpuno Awka, mutanen da aka gani basu kai guda dari ba a rumfar da ke da sama da mutane dubu masu rijista.

Sai dai kuma, Sarkin Okpuno, mai martaba Igwe S. I. Okafor (Igwe Ogene Okpuno) ya fito ya kada kuri'arsa.

Basaraken ya bukaci mutane da su fito su sauke hakkin da ya rataya a wuyansu ba tare da tsoro ba.

Masu zaben gwamnan Anambra sun yi biris, sun ki fitowa daga gidajensu don yin zabe

A baya mun kawo cewa masu yin zabe da dama sun kauracewa rumfunan kada kuri'u a zaben gwamnan Anambra da ke gudana a yanzu haka.

Wakilin Legit.ng ya ziyarci rumfunar zabe bakwai a unguwanni daban-daban a karamar hukumar Awka ta kudu, amma har zuwa misalin karfe 9:20 na safe babu masu jefa kuri'a a wuraren.

Kara karanta wannan

Anambra 2021: Jiga-jigan al'amura 10 da ya dace a sani game da zaben gwamna

Wani dan yi wa kasa hidima da ke aiki a matsayin jami'in wucin gadi a daya daga cikin rumfunar zaben da ke Aroma, ya fada ma Legit.ng cewa:

"Ga shi karfe 9 ya wuce amma bamu ga kowa ba kawo yanzu. mutane sun ki fitowa kwata-kwata."

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng