Yanzu Yanzu: Masu zaben gwamnan Anambra sun yi biris, sun ki fitowa daga gidajensu don yin zabe

Yanzu Yanzu: Masu zaben gwamnan Anambra sun yi biris, sun ki fitowa daga gidajensu don yin zabe

  • Masu kada kuri'u a zaben gwamnan jihar Anambra sun kauracewa rumfunar zabe inda suka zauna suka ki fitowa daga gidajensu
  • Wakilin Legit.ng ya ziyarci rumfunar zabe bakwai a unguwanni daban-daban amma babu masu yin zabe a wajen
  • Hakan baya rasa nasaba da fargabar da mutane ke ciki saboda tabarbarewar tsaro da aka samu a jihar a yan kwanakin nan

Anambra - Masu yin zabe da dama sun kauracewa rumfunan kada kuri'u a zaben gwamnan Anambra da ke gudana a yanzu haka.

Wakilin Legit.ng ya ziyarci rumfunar zabe bakwai a unguwanni daban-daban a karamar hukumar Awka ta kudu, amma har zuwa misalin karfe 9:20 na safe babu masu jefa kuri'a a wuraren.

Yanzu Yanzu: Masu zaben gwamnan Anambra sun yi biris, sun ki fitowa yin zabe
Yanzu Yanzu: Masu zaben gwamnan Anambra sun yi biris, sun ki fitowa yin zabe
Asali: UGC

Wani dan yi wa kasa hidima da ke aiki a matsayin jami'in wucin gadi a daya daga cikin rumfunar zaben da ke Aroma, ya fada ma Legit.ng cewa:

Kara karanta wannan

Zaben gwamna: Gwamnati ta karyata rahoton cewa mutane na tururuwan barin Anambra

"Ga shi karfe 9 ya wuce amma bamu ga kowa ba kawo yanzu. mutane sun ki fitowa kwata-kwata."

A wasu wuraren kuma, har yanzu jami'an zabe da kayayyakin zabe basu iso ba.

Mutanen Anambra da dama sun tsaya abin su a cikin gidajensu a ranar zabe sakamakon rashin tsaro da aka samu a jihar a yan kwanakin nan.

Duk da tabbacin da hukumomin tsaro suka bayar, mutanen sun kasance a cikin gidajensu saboda tsoro.

Hakazalika akwai matakan tsaro sosai a dukka yankunan da wakilin namu ya kai ziyara tare da jami'an yan sanda da na sojoji a wurare masu muhimmanci kusa da rumfunar zaben.

Zaben gwamna: Gwamnati ta karyata rahoton cewa mutane na tururuwan barin Anambra

A gefe guda, mun kawo cewa kwamishinan labarai da wayar da kan jama'a na jihar Anambra, Mista Don Adinuba, ya ce rahoton da ke yawo na cewa mutane na tururuwan barin jihar yayin da ake zaben gwamna karya ne.

Kara karanta wannan

Anambra 2021: Jiga-jigan al'amura 10 da ya dace a sani game da zaben gwamna

Adinuba ya bayyana cewa maimakon haka, mutane na shigowa cikin jihar kwansu da kwarkwatarsu, musamman wadanda suka cancanci yin zabe domin shiga sahun masu kada kuri'a a zaben gwamnan wanda ke gudana a ranar Asabar, 6 ga watan Nuwamba.

Ya magantu a kan lamarin ne a cikin wata sanarwa, wanda aka aike wa kamfanin dillancin labaran Najeriya a safiyar ranar Asabar a garin Awka, babbar birnin jihar, rahoton Daily Trust.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng