Kwankwasiyya: Naɗa ɗan shekara 66 shugaban kwamitin soshiyal midiya ya janyo cece-kuce
- Nada Muhammad Tajo Othman a matsayin shugaban kwamitin soshiyal midiya na Kwankwasiyya ya janyo cece-kuce
- Wasu daga cikin 'yan Kwankwasiyya sun nuna rashin dadinsu suna mai cewa matashi mai fada aji a soshiyal midiya ya dace a nada
- Wasu daban kuma sun ce wadanda ke ganin Othman bai dace ba, ba su san shi bane domin kwararre ne a harkar sadarwa da fasaha
Kano - Nada Muhammad Tajo Othman, tsohon jami'in kwastam dan shekara 66 matsayin shugaban kwamitin soshiyal midiya na Kwankwasiyya ya janyo cece-kuce tsakanin 'yan kwankwasiyya, rahoton Daily Trust.
Tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso shine jagorar tafiyar ta Kwankwasiyya.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Matashi ya dace a nada mukamin
Wani jigo a tafiyar, wanda ya nemi a sakaya sunansa ya shaidawa Daily Trust cewa nadin bai dace ba kuma mutane da dama ba su so hakan ba domin matashi ya dace a nada a harka ta soshiyal midiya.
Ya ce:
"Ba mu ji dadi ba. Matsayi ne da ya dace a bawa mutum mai kananan shekaru, mutumin da ke da mabiya ko fada aji a soshiyal midiya."
Da aka tambaye shi ko ba zai amince da nadin ba, amsarsa shine tsarin da aka gina tafiyar Kwankwasiyya tamkar ta sojoji ne.
Ya kara da cewa:
"Muna biyayya ga abin da shugabannin mu suka yanke, musamman Kwankwaso. Ka san, Allah ya yi wa Kwankwaso wata baiwa, idan ya yanke shawara ba a jayayya da shi. Don haka za mu amince da nadin."
Wasu sun yaba da nadin
Yayinda wasu ke nuna rashin jin dadinsu, wasu mambobin tafiyar ta Kwankwasiyya sun kare nadin a shafukan sada zumunta.
Cikin su akwai wani da yace wanda aka nada din gwani ne a bangaren fasaha sannan tsohon dan boko ne.
Ibrahim Abdulrazak Salihu ya ce:
"Ba kuskure bane idan sabon shugaban manaja ne mai kwarewa da karfin fada aji."
Shi kuma Musayyib Ungogo cewa ya yi:
"Tajo ba sabon shiga bane a soshiyal midiya, fasaha da sadarwa domin ya rike mukamin mataimakin kwantrola na kwastam da ke kula da fasahar sadarwa da sabbin dabarun zamani."
Ahmad Muntaqa na ganin cewa idan har zai iya aikin ba matsala bane. Ya ce:
"A matsayinsa na tsohon mai kula da libirari da bayanai, ya samu horaswa da zai iya aikin."
Nurudeen Isyaku Daza ya ce:
"Idan da ka san tsohon jami'in na kwastam sosai, za ka fahimci yana da kwazo da basirar sauke nauyin da aka daura masa. Abin kawai mayar da hankali ne da dagewa."
Ra'ayin Hussein idris Abdulkareem shine:
"Duk wanda Madugu ya nada ya kula da harkokin mu na soshiyal midiya da amincewarmu ne."
Martanin shugaban Kwankwasiyya Media Centre
Sanusi Bature Dawakin Tofa, shugaban cibiyar sadarwa ta Kwankwasiyya ya ce Tajo ya cancani nadin da aka masa, yana mai cewa kwararre ne a harkar.
"Duk wanda ya san Muhammad Tajo Othman zai yarda cewa ya dace da wannan nadin da aka masa. Bayan cimma nasarorin da muke gani a bangaren sadarwa a Kwastam, kwararre ne a bangaren sadarwa.
"Kwamitin wucin gadi ne ya ke jagoranta a yanzu."
Asali: Legit.ng